Hukumar jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna na tattara naira miliyan 100 duk wata

Hukumar jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna na tattara naira miliyan 100 duk wata

Mista Fidet Okhiria, Manajan Darakta na hukumar sufurin jirgin kasa, yace hukumar jirgin kasa na Abuja-Kaduna na tattara akalla naira miliyan 100 duk wata.

Okhiria ya bayyana hakan a wata hira tare da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN).

“Abun ban sha’awa ne. Zan iya fada maku cewa a yanzu da muke Magana muna samun sama da naira miliyan 100 a wata a Kaduna-Abuja.

“Bani da yawan adadin a kaina amma na san cewa akalla muna samun sama da naira miliyan 100,” inji Okhiria.

Shugaban hukumar jirgin kasan ya nuna jin dadi akan Karin fasinjoji da aka samu a AKTS, inda ya kara da cewa gwamnati na kokarin magance yawa cunkoson fasinjoji a layin dogon.

Yace: “Muna farin ciki da yadda mutane ke tururuwan zuwa sannan kamar yadda na fada a farko, da zaran mun samu sauran jirage, sannan muka fara aikin sufuri duk kowani awa guda, cunkoson zai yi kasa.

“Kamar yadda na fada ma ministan, ba wai yawan jiragen bane sai dai yawan tafiyar ne zai rage cunkoson saboda mutane daban-daban za su nemi hawa jirgin ne a lokuta mabanbanta.

“A yanzu dai, mu ci gaba da hakuri har zuwa watan Nuwamba lokacin da sabbin jiragen za su kasance a kasa.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta karrama manyan jami'an gwamnati 82

“Kuma kamar yadda nake fada ma mutane, a yanzu muna samu kula na musamman kuma hakan wani sabon cigaba ne.

“Shekaru hudu da suka gabata, babu wanda ke Maganar jirgin kasa, amma yanzu kowa, manyan mutane, masu mulki da kanana duk Magana suke kan amfani da jirgin kasa.”

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel