Wasu yan fashi 3 sun hadu da ajalinsu a hannun fusatattun matasa a jihar Benue

Wasu yan fashi 3 sun hadu da ajalinsu a hannun fusatattun matasa a jihar Benue

Wasu yan fashi da makami sun hadu da gamonsu a jiya Lahadi, 29 ga watan Satumba, yayinda wasu fusatattun matasa a suka far masu a garin Gbatse da ke karamar hukumar Ushongo na jihar Benue.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa garin Gabtse ya kasance yankin da aka gano katon kabari da wasu fitinannun makasa suka bine mutane 16 a yan kwanakin da suka gabata.

An tattaro cewa masu laifin wadanda aka bayyana sunansu a matsayin Terkaa Jabi, alias Gajere, Terkimbir Iorbunde Ahungwaor, da kuma Paul Mbailuior Damsa, sun kai mamaya a baban hanya ta garin a safiyar ranar Talata.

Idanun shaida sun bayyana cewa mutanen uku sun kai farmaki ga wasu mutane cikin mota da ke a hanyarsu ta zuwa jihar daga jihar Cross River a wani tashar bincike da baya bisa ka’ida kusa da gidan hakimin Mbayegh, Cif Nathaniel Hoyo.

An tattaro cewa basaraken ya tara matasan garin sannan a sanar da yan sanda yayinda suka bi sahun masu laifin wadanda suka tsere zuwa saman tsauni da ke yankin sannan suka boye a wani kogo.

Amma sai suka taki rashin sa’a,lokacin dsa matasa suka ma masu laifin su uku. An tattaro cewa anyi kokarin dakatar da fusatatten matasan wadada suka dunga jifan masu aifin da duwatsu.

Idanun shaida sun bayyana cewa a cikin haka ne aka kasha matasan sannan aka ja su zuwa hanya kafin yan sanda suka dauke gawawwakisu sannan suka baza su a ofishin yan sandan Ushongo.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta karrama manyan jami'an gwamnati 82

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan Benue, Catherine Anene, yayi bayanin cewa yan sandan na musayar wuta d yan fashin ne okacin da suka haye saman tsaunin sanan suka boye a wani kogo.

Anene ya kara da cewa a lokacin binciken yan fashin, fusatattun matasan suka gano su kafin yan sanda sannan suka kashe su, amma yan fashin sun harbi daya daga cikin matafiyan da farin wanda a yanzu yake samun kulawar likitoci.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel