Cigaba da garkame Sowore cin zarafi ne kuma ya sabawa doka - NBA

Cigaba da garkame Sowore cin zarafi ne kuma ya sabawa doka - NBA

Kungiyar NBA ta Lauyoyin Najeriya, ta yi Allah-wadai da sabawa umarnin kotun tarayya da ke Abuja da hukumar tsaro ta DSS masu fararen kaya su ka yi a kan a bada belin Omoyele Sowore.

Duk da Alkali ya nemi DSS ta saki Omoyele Sowore bisa beli, hukumar tsaron ta yi kememe ta ki bin wannan umarni na shari’a. A dalilin wannan Lauyoyin Najeriya su ka fitar da wani jawabi jiya.

A Ranar Asabar, 29 ga Watan Satumba, Sakataren yada labarai na kungiyar NBA na kasa, Kunle Edun ya fitar da jawabi ya na mai tir da keta hakki da alfarmar Omoyele Sowore da DSS su ke yi.

Edun yake cewa: “DSS ta na kara jawowa kanta wannan bakin sunan da ta yi wajen watsi da hukuncin shari’a da gadara, musamman wajen sabawa umarnin kotu wajen kare hakkin jama’a.”

NBA ta ce cigaba da rike Omoyele Sowere da DSS ta ke yi ya zama cin zarafi ga martabarsa don haka ta nemi hukumar DSS ta yi maza ta bi umarnin da kotu ta yi a Ranar 24 ga Satumban 2019.

KU KARANTA: Osinbajo zai kai ga ci a Najeriya inji Tunde Bakare

A jawabin Lauyoyin kasar da ke lemar kungiyar NBA sun kuma nemi gwamnati ta saki duk wani wanda yake rike a hannun DSS ba tare da an maka shi kotu da sunan ya aikata ko wani laifi ba.

Har ila yau, a daidai wannan lokaci, wani fitaccen masanin yau da gobe, Ishmael Rufus, ya yi kira ga Alkalai su daina watsi da sha'anin tsaron kasa wajen kare hakkin kankin wani mutum guda.

Fiye da kwanaki 50 kenan Sowore ya na hannun hukuma inda ake zarginsa da manyan laifuffuka har da zagin shugaban kasa. Sai dai kotu ta ce a bada belinsa, amma jami'an DSS sun yi mursisi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel