Najeriya tana asarar N5trn a duk shekara ta hanyar satar mai

Najeriya tana asarar N5trn a duk shekara ta hanyar satar mai

- Majalisar wakilai ta fadin adadin dukiya da Najeriya ta ke asara a duk shekara ta hanyar satar mai

- Dan majalisa mai wakilcin mazabar Aguata ta jihar Anambra, Honarabul Chukwuma Umeoji, shi ne ya bayyana hakan

- Umeoji ya ce Najeriya tana asarar adadin dukiya ta kimanin Naira tiriliyan 5 ta hanyar satar mai a duk shekara

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, Najeriya tana asarar dukiya ta kimanin naira tiriliyan biyar a duk shekara sanadiyar satar danyen mai daga bututan da ke fadin kasar nan.

Wannan rahoto na kunshe cikin wata sanarwa da dan majalisar tarayya mai wakilcin mazabar Aguata ta jihar Anambra, Honarabul Chukwuma Umeoji, ya gabatar a ranar Alhamis kamar yadda kafar watsa labarai ta Channels TV ta ruwaito.

Hakazalika Umeoji ya ce, a yankin Neja Delta kadai cikin shekarar da muke ciki, an sace kimanin ganguna miliyan 22 na danyen mai wanda darajarsa ta kai kimanin naira tiriliyan 1.3.

KARANTA KUMA: Da kudaden talakawa wasu gwamnonin Najeriya suka biya aikin Hajji

'Dan majalisar ya ce baya ga durkusar da tattalin arzikin kasa, satar danyen mai tana haddasa lalacewar zamantakewa, lamarin da yace ya kai intaha.

A sanadiyar wannan lamari ya sanya majalisar wakilai ta kafa wani kwamiti domin gudanar da bincike a kan adadin danyen mai da ake sacewa a kasar.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel