Da kudaden talakawa wasu gwamnonin Najeriya suka biya aikin Hajji

Da kudaden talakawa wasu gwamnonin Najeriya suka biya aikin Hajji

A wani rahoto da Muryar Duniya ta wallafa a ranar 30 ga watan Satumba, wani binciken kwa-kwaf ya nuna cewa, a bana duk da cewa akwai wadanda basu sauke nauyin bashi na albashin ma'aikata ba, an samu wasu gwamnonin Najeriya da suka batar da biliyoyin kudi daga baitul malin talakawa domin daukar nauyin mahajjata zuwa sauke farali a kasar Saudiya da kuma masu kai ziyarar ibada a birnin Kudus.

Bankadar da jaridar Daily Trust ta yi na nuni da cewa, cikin wadanda gwamnonin suka dauki nauyinsu zuwa kasar Saudiya, da kuma birnin Kudus na kasar Isra'ila sun hadar da malaman addinai, jami'an gwamnati, 'yan siyasa, jami'an kiwon lafiya, 'yan uwa da kuma makusanta.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, ya zuwa yanzu akwai gwamnoni da dama da suka gaza sauke nauyin hakkin ma'aikatansu duk da irin makudan kudade na tallafi da suka karba daga hannun gwamnatin tarayy da manufar biyan albashi da kuma sallamar masu karbar fansho.

Hakazalika bankadar ta kuma gano yadda da yawa daga cikin gwamnonin da suka dauki nauyin mahajjatan suka yi watsi da wasu muhimman ayyukan ci gaban al'umma da ke bukatar kulawa ta musamman.

KARANTA KUMA: EFCC ta kama masu zamba ta yanar gizo 6 a birnin Abuja

Ana iya tuna cewa, a bana dai kudin kujerar aikin hajji ta kowane mutum daya ta kai kimanin naira miliyan 1.5 yayin da kujerar masu zuwa ziyarar ibada a birnin Kudus ta kai kimanin naira dubu dari bakwai da goma.

Hukumar jin dadin alhazai ta Najeriya NAHCON, ta tabbatar da cewa kimanin musulman Najeriya fiye da dubu 65 ne suka sauke farali yayin hajjin bana a kasar mai tsarki.

Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel