EFCC ta kama masu zamba ta yanar gizo 6 a birnin Abuja

EFCC ta kama masu zamba ta yanar gizo 6 a birnin Abuja

Jami'an reshen kula da masu aikata miyagun laifuka ta yanar gizo na hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati EFCC, a ranar Litinin sun samu nasarar cafke wasu mutasa 6 masu zamba ta intanet wanda aka fi sani da Yahoo boys.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, hukumar EFCC ta cafke ababen zargin shida ne a wani gida mai lamba 1 da da kuma wani gidan mai lamba 3 a unguwar da ke babban birnin kasar nan na tarayya wato Abuja.

Jerin matasa 6 da hukumar EFCC ta kama masu zamba ta yanar gizo a birnin Abuja
Jerin matasa 6 da hukumar EFCC ta kama masu zamba ta yanar gizo a birnin Abuja
Asali: Twitter

Rahoton na kunshe a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya gabatar yayin zantawa da manema labarai a yau Litinin, lamarin da ya ce ya biyo bayan wani bincike da leken asiri da aka gudanar a yankin na wani lokaci takaitacce.

Sanarwar babban jami'in hukumar EFCC ta bayyana sunayen 'yan damfaran da suka shiga hannu da suka hadar da Raphel Chibuzor, Oyewumi Adewale, Onyeogheni Isioma Progress, Ayo Abiodun Richard, Oloyede Faith Damilare da kuma Ibrahim Yusuf Waziri.

KARANTA KUMA: Murnar cikar Najeriya shekaru 59 da samun 'yancin kai: Gwamna Fintiri ya gafarta wa Fursunoni 18 a jihar Adamawa

Wadansu daga cikin ababe da aka samu a hannun miyagun masu ta'adar ta halasta kudin haramun sun hadar da wayoyin salula, kwamfutocin tafi da gidanka, da kuma motoci na alfarma samfurin Toyota Highlander da Corolla.

Mista Wilson ya ce za a gurfanar da su gaban kuliya da zarar bincike ya kammala.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel