Tabbas akwai damuwa a ofishin mataimakin shugaban kasa Osinbajo - SMBLF

Tabbas akwai damuwa a ofishin mataimakin shugaban kasa Osinbajo - SMBLF

Wata kungiya ta shugabannin Kudu da kuma yankin tsakiyar Najeriya, SMBLF, a ranar Lahadin da ta gabata ta kaddamar ta cewa, tabbas akwai babbar damuwa a ofishin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, biyo bayan takaddamar da ta kunno kai dangane da ofishin nasa kwanaki kadan da suka gabata.

A sanadiyar haka kungiyar ta bukaci fadar shugaban kasa da ta fito karara ta bayyana abin da ta ke nufi a kan mataimakin shugaban kasar ko kuma ta gaggauta mayar masa da karfin ikon da a baya ya rataya a wuyansa.

Wannan bukata na zuwa ne a yayin da shugabannin kungiyar suka fidda wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai a birnin Ikko na jihar Legas, inda suka ce rage wa mataimakin shugaban kasa karfin iko a kasar na wasu nauye-nauye wanda a baya suka rataya a wuyansa na cin karo da ambaton gwamnonin jam'iyyar APC wanda suka ce babu wani zaman doya da manja da ake yi a fadar shugaban kasa.

Kungiyar SMBLF cikin wata sanarwa da ta gabatar da sa hannun shugabanninta, Cif Edwin Clark, Pa Ayo Adebanjo, Cif John Nwodo, da kuma Dr. Pogu Bitrus, sun nemi fadar da shugaban kasa da ta tabbatar a karfin ikon da rataya a ofishin mataimakin shugaban kasa da a cewar su an samu akasin haka makonni biyu da suka gabata.

Kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito, kungiyar a yayin fadar shugaban kasa da ta bayyana abin da ke faruwa da ofishin Farfesa Osinbajo, ta ce tabbas wannan manuniya da ke haskaka wata babbar damuwa a ofishin mataimakin shugaban kasar duk da ba su kai ga sanin irin nau'inta ba.

KARANTA KUMA: Sowore: Dalilin da ya sa Buhari ba zai sa baki ba a yanzu - Adesina

Ana iya tuna cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari makonni kadan da suka gabata ya kaddamar da majalisar bai wa shugaban kasa shawara kan tattalin arziki biyo bayan rushe kwamitin tattalin arzikin kasar, wanda mataimakin shugaban kasa Osinbajo ke jagoranta.

Jaridar BBC Hausa ta ruwaito cewa, yayin da wasu ke yi wa lamarin sambarka, wasu dai na kallon matakin a matsayin yunkurin rage ikon mataimakin shugaban kasar.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel