Sowore: Dalilin da ya sa Buhari ba zai sa baki ba a yanzu - Adesina

Sowore: Dalilin da ya sa Buhari ba zai sa baki ba a yanzu - Adesina

A ranar Lahadin da ta gabata ne fadar shugaban kasa ta ce, shugaba Muhammadu Buhari ba zai iya shiga cikin takaddamar mawallafin jaridar Sahara Reporters ba, Omoyele Sowore, wanda hukumar 'yan sandan farin kaya DSS ke ci gaba da tsarewa.

Fadar shugaban kasa kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito ta bayyana cewa, Buhari ba zai gaggauta tsoma bakinsa ba kan ci gaba da tsare Mista Sowore wanda ke hannun hukumar DSS, lamarin da ta ce sanya baki a yanzu ya yi wuri.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, shi ne ya bayyana hakan yayin tsokaci dangane da tsohon dan takarar shugabancin kasar nan na jam'iyyar AAC wanda hukumar DSS ke ci gaba da tsare duk da umarnin kotu na sabanin haka.

Mr Adesina, yayin tofa albarkacin bakin sa dangane da shirin siyasa na ranar Lahadi wanda kafar watsa labarai ta Channels TV ta saba shiryawa, ya ce a halin yanzu shugaba Buhari zai yi gaggawar sa baki dangane da ci gaba da tsare dan gwargwarmaya Sowore wanda hukumar tsaron cikin gida DSS ke yi bayan hukuncin da kotu ta zartar na umarnin sakin sa.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai dangane da dalilai da suka sanya hukumar DSS ta ki yi wa umarnin kotu da'a na sakin Sowore, Mista Adesina ya ce wannan hurumi ne da ya shafi kotun shari'a da kuma hukumar tsaron wanda kakakinta, Peter Afunanya ya fi dacewa ya bayar da amsoshi.

Ya ce a halin da ake ciki bai kamata ba fadar shugaban kasa ta tsoma bakinta cikin takaddamar Mista Sowore, lamarin da ya ce muddin ta aiwatar da hakan za tayi aiki na gaggawa wanda bai dace da ita ba.

KARANTA KUMA: Dole ne gwamnati ta karo hanyoyin hana matasa zaman kashe wando - Rabaran George

Ana iya tuna cewa, a ranar 24 ga watan Satumba ne wani alkalin babbar kotun tarayya dake zamanta a garin Abuja, Taiwo Taiwo, ya bai wa hukumar DSS umarnin sakin Mista Sowore bayan ya cika duk wasu sharuda na beli, sai dai kuwa ya zuwa yanzu kwanaki shida kenan da wannan umarnin babu amo ballantana labarin sakinsa.

Babu shakka Mista Sowore ya shiga hannun jami'an hukumar DSS a ranar 3 ga watan Agusta bayan zarginsa da kulla aniyar jagorantar zanga-zangar juyin juya hali a kan maudu'in #RevolutionNow ta nuna rashin amincewa da salon mulkin Buhari.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel