Mayakan Boko Haram sun kashe mutane dama a garuruwan Borno

Mayakan Boko Haram sun kashe mutane dama a garuruwan Borno

Muhukunta sun ruwaito cewa, rayukan mutane da dama wanda ba a iya tantance adadinsu ba sun salwanta a yayin da daruruwan mutane suka tsere daga muhallansu biyo bayan wani bakin gumurzu da ya auku tsakanin dakarun sojin Najeriya da kuma mayakan kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram a garin Gubio.

Jaridar Daily Tryust ta tattaro cewa, da misalin karfe 4.40 na Yammaci mayakan Boko Haram cikin wani babban ayari suka isa garin Gubio da ya kasance babban gari na karamar hukumar Gubio ta jihar Borno, inda suka rinka harbe-harben harsashi na bindiga kan mai Uwa da Wabi.

Majiyar rahoton wadda ta kasance ta jami'an tsaro ta zayyana cewa, an shafe tsawon kimanin sa'o'i uku ana tafka bakin gumurzu tsakanin mayakan Boko Haram da dakarun tsaro wadda su ma lamarin ya zo masu a bazata, sanadiyar kwanton bauna da 'yan ta'addan suka yi.

Babu shakka rayuka da dama sun salwanta daga bangarorin biyu, a yayin da adadin mayakan Boko Haram da suka kawo harin ya dara na jami'an tsaro da kuma mafarauta 400 da ke jiran ko ta kwana.

Sai dai majiyar ta ce dakarun tsaro sun nuna bajintar gaske wajen dakile harin a yayin da mayakan Boko Haram da damu suka raunata kuma suka tsere da kafafunsu sanadiyar ingancin makaman dakaru da ya yi wa na su fintinkau.

KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta karrama manyan jami'an gwamnati 82

A wani rahoton mai nasaba da wannan, dakarun tsaro na Operation Lafiya Dole tare da hadin gwiwar hukumar hana fasakwauri ta Najeriya, sun samu nasarar cafke wani matashi da daruruwan babura a kan babbar hanyar Moguno da ake zargi dan Boko Haram ne.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel