An kwace motoci 25 a hannun dan shugaban kasa kuma mataimakin mahaifinsa a kasar Afrika

An kwace motoci 25 a hannun dan shugaban kasa kuma mataimakin mahaifinsa a kasar Afrika

An fara gwanjon tarin wasu motocin alfarma mallakar mataimakin shugaban kasar Equatorial Guinea, Teodorin Obiang, ranar Lahadi a kasar Switzerland. An yi kiyasin cewa darajar motocin zai kai kudin miliyan 15 na Swiss frans, kimanin dalar Amurka miliyan $18.7.

"Wannan gwanjon motoci na musamman ne, motoci ne na alfarma da ko kadan basu sha wahala ba," Philiph Kantor, mai sayar da kayayyaki a nahiyar Turai ya sanar da kamfanin dillancin labarai na AFP.

Daga cikin motocin Obiang da aka saka a kasauwa ga masu rabo akwai Ferrari guda 7, Lamborghini guda uku, Bentley guda 5, Maserati da McLaren.

Mafi tsada a cikin motocin sun hada Lamborghini Veneno Roadster, wacce aka yanke farashinta a kan Yuro miliyan 4.8m da 5.7m da kuma wata Ferarri ta musamman mai launin ruwan dora wa, wacce aka yanke wa farashi a kan Yuro miliyan 2.4 zuwa 2.6m.

Sashen shari'a na kasar Swiss ne ya kwace motocin daga hannun Obiang, mai jiran gadon mulkin kasar Equatorial Guinea, bayan sun fara tuhumarsa da laifin almundahanar kudade.

DUBA WANNAN: Masu yi don Allah: Wani mutum ya bayar da gudunmawar $1m ga cibiyar Sheikh Ibrahim Saleh, ya nemi a boye sunansa

Maihaifin Obiang, shugaba Teodoro Obiang Nguema, ya shafe shekaru 40 a kan karagar mulkin kasar Equatorial Guinea.

A cikin watan Fabrairu ne masu gurfanar da Obiang suka bayyana cewa sun janye tuhumarsa da badakalar kudi, amma kuma sun kwace motocinsa na shari'a.

Ana yawan samun Obiang da laifin almubazzaranci da kudin jama'a, musammam wajen sayen motocin alfarma masu tsada da gina gidaje masu kawa.

Ko a cikin watan Satuma, sai da kafafen yada labarai a Brazil suka bayyana cewa jami'an 'yan sanda da na kwastam a kasar sun kwace wata jaka dake dauke da miliyan $16 a hannun daya daga cikin 'yan rakiyar Obiang yayin wata ziyara da ya kai kasar Brazil.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel