Ana wata ga wata: Mahaifin da ya daure 'yayansa 2 da sasari na tsawon shekara 2 ya mutu a hannun hukumar NAPTIP

Ana wata ga wata: Mahaifin da ya daure 'yayansa 2 da sasari na tsawon shekara 2 ya mutu a hannun hukumar NAPTIP

Malam, Muhammadu Ujudud, mutumin da ya saka diyarsa da dansa a mari na tsawon shekaru biyu, ya mutu a hannun hukumar yaki da safarar yara da bautar da su (NAPTIP), reshen jihar Kano.

Da yake tabbatar da mutuwar Ujudud, kwamandan hukumar NAPTIP a Kano, Alhaji Shehu Umar, ya ce mutumin ya mutu ne a asibitin Murtala Muhammad da ke birnin Kano.

Umar ya ce, "an kawo mana mutumin ofishinmu da misalin karfe 6:00 na yamma, bayan an kawo shi sai ya nemi izinin cewa zai je ya yi fitsari, kuma a can wurin da zai yi fitsarin ne ya yanke jiki ya fadi. Nan da nan muka garzaya da shi asibiti, inda ya mutu yayin da ake duba lafiyarsa.

"Da ma matarsa ta sanar da mu cewa yana da ciwon zuciya, mutumin na fama da hawan jini da ciwon zuciya," a cewarsa.

Kwamandan na NAPTIP ya bayar da tabbacin cewa hukumarsu zata cigaba da binciken lamarin daure yaran da marigayin ya yi har na tsawon shekara biyu, tare da bayyana cewar mutuwarsa ba zata hana su cigaba da binciken ba.

DUBA WANNAN: Miji, mata da jaririnsu sun mutu a cikin gidansu da wasu suka saka wa wuta a Kano

"Za mu koma kauyen domin neman bayanai a kan halayyar mutumin da kuma binciken dalilin da yasa ya daure 'ya'yansa. Mutuwarsa ba zata hana mu cigaba da bincike ba," a cewarsa.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa jami'an hukumar NAPTIP sun kama mutumin ne a kauyen Rinji da ke karkashin karamar hukumar Madobi a jihar Kano bisa zarginsa da daure 'ya'yansa biyu da sarka har na tsawon fiye da shekaru biyu, saboda gurbacewar tarbiyyarsu.

A yayin da ake zargin cewa mutumin ya daure diyarsa mace saboda ta ki yarda da auren dole, ana zargin cewa ya daure dansa namiji saboda tu'ammali da miyagun kwayoyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel