A je, a dawo, Osinbajo zai kai ga ci a Najeriya – Tunde Bakare ya sake hasashe

A je, a dawo, Osinbajo zai kai ga ci a Najeriya – Tunde Bakare ya sake hasashe

Babban Limamin cocin nan na Latter Rain Assembly, Fasto Tunde Bakare ya bayyana abin da zai faru ga mataimakin shugaban kasan Najeriya watau Farfesa Yemi Osinbajo.

Fasto Tunde Bakare ya yi wannan jawabi ne a Ranar 29 ga Watan Satumba 2019, inda ya ce mataimakin shugaban kasar zai tsallake duk wasu matsaloli da su ke bijiro masa.

Da ya ke jawabi a jiya Asabar, babban Malamin na Kirista ya ce: “Mataimakin shugaban kasa Osinbajo zai ba marada kunya a karshe. Ku na tunanin cewa ni Sakarai ne?”

Tsohon ‘dan takarar mataimakin shugaban kasar na Najeriya ya kara da cewa: “Sai dai idan har shi (mataimakin shugaban kasar) ya sabawa rantsuwar ofis din da ya dauka."

KU KARANTA: Bakare ya ce zai zama Shugaban kasa bayan Buhari

Jaridar The Nation ta rahoto Malamin addinin ya na wannan jawabi ne a matsayin martani kan rahoton da aka rika yadawa a baya na zargi kan mataimakin shugaban kasar.

Wani ‘dan adawa a kasar nan ya fito ya na zargin mataimakin shugaban kasa Osinbajo da karbar Naira biliyan 90 daga hannun hukumar FIRS domin yi wa jam’iyyar APC aiki.

Hukumar FIRS mai karbar haraji a Najeriya ta karyata wannan rade-radi na cewa ta ba APC kudin yakin neman zabe. Tuni dai Osinbajo ya karyata wannan da cewa zai je kotu.

A baya ana zargin cewa mataimakin shugaban na Najeriya ya na cikin wani hali na tarka-tarkar siyasa. Bakare wanda ya ce zai karbi mulki ya ce babu ruwansa da wannan surutai.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel