Buhari da Ramaphosa za su shawo kan rikicin kasar Afrika ta Kudu - Inji Obasanjo

Buhari da Ramaphosa za su shawo kan rikicin kasar Afrika ta Kudu - Inji Obasanjo

Tsohon shugaba Olusegun Obasanjo, ya shawarci ‘yan Najeriya da su ka tsero daga kasar Afrika ta Kudu a dalilin harin da aka rika kai wa baki da masu ci-rani da su yi niyyar komawa aikinsu.

Cif Olusegun Obasanjo yace ‘Yan Najeriyar su ka baro kasar Afrikan su fara shirin komawa wuraren neman abincin na su. Hakan na zuwa ne bayan rigimar da aka yi ta yi kwanaki ta lafa.

Obasanjo ya bayyana wannan ne domin ya na sa ran zaman da za ayi tsakanin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da kuma Takawarnsa Cyril Ramaphosa na Afrika ta Kudu zai kawo mafita.

Shugabannin manyan kasashen Nahiyar za su gana ne a cikin Wata mai zuwa wanda tsohon shugaban na Najeriya ya fara hangen za a warware duk wasu matsaloli da kasashen su ka shiga.

Cif Obasanjo ya yi wannan jawabi ne lokacin da ya ke magana da masu daukar rahoto a gidansa da ke Garin Abeokuta a jihar Ogun a kan yadda tattaunawarsa da shugaba Ramaphosa ta kaya.

Obasanjo ya ke fadawa ‘yan jarida cewa: “Na nemi amfani da damar zuwa Afrika ta Kudu domin in ziyarci shugaban kasa Cyril Ramaphosa, kuma na samu wannan dama ba tare da bata lokaci ba.

KU KARANTA: An soma murnar cikar Najeriya shekaru 59 da 'yancin kai

“Daga cikin abubuwan da mu ka tattauna akwai batun harin da ake kai wa Baki da sauran Bakaken fatar Afrika a Afrika ta Kudu. Shugaban kasar ya nuna mani cewa lallai, an yi kuskure.”

Janar Obasanjo ya kara da cewa: “Shugaban ya fada mani cewa idan mun yi kuskure, dole mu gyara. Ina tunanin wannan kalamai ne masu kyau kuma na san cewa shugaban da gaske yake yi.”

A cewar tsohon shugaban, Ramaphosa ya tambayesa game da yadda za a kawo karshen rikicin. Bayan nan shugaban kasa Afrika ta Kudu ya yi kira ga jama’ansa su daina taba ‘yan ci-rani.

Janar din ya na ganin ya kamata ‘yan Najeriya su yi azamar komawa wannan kasa domin Cyril Ramaphosa ya shirya magance matsalar, bayan zaman da zai yi a farkon Oktoba da Buhari.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel