Buhari: Tsarin mulki bai ce in nada Osinbajo lokacin da na yi tafiyan Afrilu ba

Buhari: Tsarin mulki bai ce in nada Osinbajo lokacin da na yi tafiyan Afrilu ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kare kansa a game da kin nada Mataimakinsa Yemi Osinbajo da ya yi a matsayin Mukaddashin shugaban kasar Najeriya lokacin da shi ba ya kasar.

Shugaba Buhari yake cewa babu inda dokar kasar Najeriya tace dole sai Mataimakin shugaban kasa ya karbi ragamar mulki idan har shugaban kasa zai yi tafiyar da ba ta zarce kwanaki 21 ba.

Shugaban kasar ya yi wannan bayani ne da ya ke shirin kare kansa bayan karar da wani Lauya Inibehe Effiong ya shigar a kotu ya na mai kalubalantar shugaban kasar da Ministan shari’a.

Wannan kara mai lamba FHC/L/CS/763/2019 na gaban Alkali mai shari’a A.O Faji na babban kotun tarayya da ke Legas. Ana sa rai za a saurari karar gobe Litinin, 30 ga Satumban 2019.

Mai karar ya na so kotu ta fitar da matsaya kan ko shugaban kasa ya na iya tafiya ba tare da ya nemi majalisa ta san cewa mataimakinsa zai karbi aikinsa ba a daidai wannan lokaci ba.

KU KARANTA: Hadimin Uwargidar Buhari ya yi magana kan rade-radin rikici a Aso Villa

Buhari ya rubuta na sa raddin domin kare kansa inda yace tsarin mulki ya ce shugaban kasa ya sanar da shugaban Sanatoci da Kakakin majalisa nadin mukaddashi ne idan zai dade a waje.

Lauyan yake cewa dokar Najeriya ta bada sharadin cewa shugaban kasa ya mikawa Mataimakinsa mulki ne kurum idan har tafiyar da zai yi a wajen ofis zai dauki akalla kwanaki 21.

Shugaban kasar ya rubuta martani ne ta bakin wani Lauya da ke aiki a sashen kara na ma’aikatar shari’a. Lauyan ya sanar da kotu cewa kwanaki 9 rak shugaban kasar ya yi ba ya ofis a Afrilu.

Lauyan gwamnatin ya nemi ayi fatali da wannan kara domin ba ta da madogara. A cikin watan Afrilun bana Buhari ya dauki hutu inda ya tafi Birtaniya ba tare da Osinbajo ya karbi mulki ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel