Ku daina yi wa mutumin da zai kara aure wa'azi, Sarki Sanusi ya bawa shugabannin arewa muhimmiyar shawara

Ku daina yi wa mutumin da zai kara aure wa'azi, Sarki Sanusi ya bawa shugabannin arewa muhimmiyar shawara

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya ce Najeriya kan iya cimma muradun cigaban kasa bisa tsarin majalisar dinkin duniya (SDGs) ta hanyar bawa ilimin yara mata fifiko.

Da yake bayar da shawara ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, gwamnonin yankin arewa da sauran masu ruwa da tsaki a kan taron wakilan mambobin majalisar majalisar dinkin duniya (UNGA) da aka yi a kasar Amurka, Sanusi II ya ce mutumin da ke son kara aure ba ya jin wa'azi, tare da bayyana cewa ilimantar da yara mata ne kawai mafita.

Sanusi ya ce akwai banbanci ta fuskar yadda za a cimma muradun SDGs a yankin kudu da arewa tare da bayyana cewa ilimantar da yara mata ne abinda ya kamata gwamnonin arewa maso yamma da arewa maso gabas su fi bawa fifiko."

"Idan zan bawa gwamnonin yankin arewa maso yamma da arewa maso gabas shawara guda daya a kan abinda ya kamata su fi bawa muhimmaci domin cimma muradun MDGs, ta ce su ilimantar da 'ya'ya mata," a cewar Sanusi II.

DUBA WANNAN: Jaruman Kannywood da suka barranta kansu da tsarin hukumar tace fina-finai a Kano

Sarki Sanusi II ya cigaba da cewa; "ku kalli arewa da irin kalubalen da yankin ke fuskanta a bangaren tattalin arziki da sauransu. Adadin mutanen mu na hauhawa koda yaushe, yawanmu na ninka wa duk bayan shekaru 20 zuwa 25.

"Albarkatun da jama'a suka dogara da su sai janye wa suke, suna koma wa baya a yayin da yawan al'umma ke kara yawa. Duk kudin da gwamnati zata kashe ba zai warware matsalolin m ba.

"A gyara wasu al'adu da suka shafi auratayya, musamma aurar da kananan yara mata. Ba kudi bane ke sa mutanen mu auren mata barkatai - ba maganar kudi ba ce."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel