Tsoffin jami'an gwamnatin tarayya na cikin tashin hankali akan kwangilar da ta jefa Najeriya a bashi

Tsoffin jami'an gwamnatin tarayya na cikin tashin hankali akan kwangilar da ta jefa Najeriya a bashi

- Tsoffi jami'an gwamnati da kuma wasun da suke aiki yanzu na cikin zullumi da tashin hankula

- A koyaushe za a iya bukatar tattaunawa ko gurfanar da wadanda ke da hannu a kwangilar P&ID da ta jefa Najeriya a bashin $9.6bn

- Gwamnatin tarayya na kokarin ganin a kara duban shari'ar inda majalisar wakilai da hukumar yaki da rashawa ta EFCC ke kokarin zakulo masu hannu a aika-aikar

A halin yanzu, jami'an gwamnati da tsoffin jami'an na cikim tsoron binciken hukuncin bashin kamfanin P&ID da aka yankewa Najeriya.

Gwamnatin tarayya ta garzaya kotun turai don kawo maslaha akan bashin. 'Yan majalisar wakilai da hukumar yaki da rashawa ta EFCC na bincikar yadda abin ya kasance.

An gano cewa, masu bincike na ta zakulo bayanai akan kwangilar.

"Masu bincike a kullum na cikin gano wadanda aka hada kai dasu wajen take dokokin cikin gida da na kasashen duniya akan kwangilar. Za a iya amfani da binciken wajen gurfanar da wadanda suka karya dokar har ta kai ga wannan badakalar," in ji wata majiya mai karfi.

KU KARANTA: Tarihin-kadan-daga-cikin-jaruman-kannywood-masu-tasowa

An gano cewa kuma, hukumar yaki da rashawa ta shirya don gurfanar da tsoffin ma'aikatan gwamnatin tarayya na lokacin.

Tsohon mataimaki na musamman ga shugaban kasa ya sanar da jaridar The Nation cewa, zargin da hukumar rashawa ke wa wasu jami'an gwamnati zai iya bankado sirrika da yawa.

Ya ce: "Dukkanmu jira muke mu ga abinda zai faru. Matsalar P&ID zata iya zama wata dama da wasu mutane ke jira don kai wasunmu kasa. Lokacin magana bai yi ba amma zan iya sanar da ku cewa duk a tsorace muke."

Wata majiya kuma, tsohon mataimaki na musamman ga wani minista ya ce: "Shari'a da bincike akan P&ID ta isa ta sanya mutane da dama cikin tashin hankali. An gano sunayen masu hannu a ciki kuma bincike na cigaba. Kowa a tsorace yake. Mun yi aiki ne a wancan lokacin da umarni da aka bamu."

An gano cewa, hukumar EFCC na cigaba da gano jami'an gwamnati da ke da hannu dumu-dumu cikin taimakon kamfanin don cutar da kasar.

Majiya mai karfi ta ce, za a cigaba da gayyatar mutane don amsa tambayoyi saboda hukumar da kara gano wasu tsoffin jami'an gwamnatin da ke da hannu a ciki.

"Abinda zan iya cewa shi ne, wannan cutar ta hadin kai ce. An tsara duk yadda za a yi tun kafin ma a sa hannu a kwangilar. Wadanda suka aikata hakan ina da tabbacin sun san kansu kuma sun tsammanin za a zo kansu." In ji majiyar.

A halin yanzu, kakakin majalisar dattawa, Femi Gbajabiamila ya nada kwamitin da zata binciko kulalliyar da ke cikin kwangilar.

Jaridar The Nation ta gano cewa, kwamitin na ta tuhumar wasu mutanen da ta san da hannunsu a ciki. Hakan kuwa na daga cikin aikin kwamitin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel