NDLEA ta gargadi matasa a kan shakar warin da ke fito wa daga masai ko kwatami saboda su bugu

NDLEA ta gargadi matasa a kan shakar warin da ke fito wa daga masai ko kwatami saboda su bugu

Kwamandan hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a jihar Gombe, Aliyu Adole, ya gargadi matasan jihar a kan su guji shakar warin da ke fito wa daga cikin masai da kwatami don kawai su bugu.

Shugaban na NDLEA ya ce wasu matasa sun bullo da wata sabuwar halayya ta shakar warin da ke fito wa masai da kwatami domin su bugu.

Adole ya bayyana hakan ranar Asabar yayin da yake gabatar da jawabi a wurin wani taro da kungiyar masana kimiyyar magani (Pharmacists) suka shirya domin fadakar da matasa a kan illolin tu'ammali da miyagun kwayoyi.

"Wannan taro ne na yaki da shan miyagun kwayoyi. Ku na iya hada kai da NDLEA domin yaki da shan miyagun kwayoyi, mu kuma za mu baku dukkan goyon bayan da kuke bukata. Babu wani lokaci mafi dace wa da ya kamata a tashi tsaye domin yaki da shan kayan maye kamar yanzu" a cewarsa.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya yi furuci a kan bankado wani gida da aka daure kananan yara 300 a Kaduna

Jagoran matasan da suka shirya taron, Shadrach Nziomisaki, ya ce jihar Gombe na daga cikin jihohin dake da yawan mata masu amfani da kayan maye.

A cewar mataimakin kwamandan NDLEA a jihar Gombe, Okafor Olisaemeka, amfani da miyagun kwayoyi na kara yawan aiyukan ta'addanci da suka hada da fashi da makami da fyade.

"Wasu na soya kyankyaso tare da hada shi da wasu abububan, wasu na tattara audugar nade jinin al'ada ta mata tare da sarrafa su domin shaye-shafe. Wanda ya bugu zai iya aikata kowanne irin laifi, saboda bai san inda kansa yake ba," a cewar Okafor.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel