NCC ta datse sadarwar layukan waya miliyan 2 a Najeriya

NCC ta datse sadarwar layukan waya miliyan 2 a Najeriya

Muryar Duniya ta ambato gwamnatin Najeriya a yayin da ta bayar da sanarwar katse layukan sadarwa na wayar hannu kimanin 2,227,311 marasa rijista ko kuma rashin cika ka'idodin yi wa layuka rijista.

Wannan mataki da gwamnatin kasar ta dauka na zuwa ne a sanadiyar umarnin da ministan sadarwa na kasar, Dakra Isa Ali Pantami ya bai wa hukumar lura da harkokin sadarwa ta Najeriya NCC.

Ana iya tuna cewa, a ranar 12 ga watan Satumban da ta gabata ne ministan kasar ya bai wa hukumar NCC umarnin rufe duk wasu layukan waya da ba su da rijista.

Ministan na sadarwa ya alakanta gibin da aka samu wajen rijistar layukan waya barkatar ba tare da ka'ida ba da tabarbarewar tsaro a Najeriya musamman ta'addancin masu garkuwa.

Jaridar BBC Hausa ta ambato ministan yana cewa, ci gaba da yaduwar miyagun laifuka na ta'addanci musamman ta'adar garkuwa na da nasaba mai girman gaske dangane da kuskuren da aka samu a bangaren sadarwa.

KARANTA KUMA: An binne gawar Mugabe a kauyen Kutama

Dakta Pantami ya ce kimanin kaso 90 na miyagun laifuka da ake tafkawa a kasar na aukuwa ne da mafi girman taimako na wayoyin hannu musamman ta'adar masu garkuwa da mutane da ta addabi kasar.

A sanadiyar haka ministan ya ce ma'aikatarsa ta sadarwa za ta jajirce wajen tallafa wa hukumomin tsaro a fannin dakusar da kaifin aukuwar miyagun laifuka ta hanyar rufe dukkanin layukan waya marasa rijista.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel