An binne gawar Mugabe a kauyen Kutama

An binne gawar Mugabe a kauyen Kutama

Biyo bayan takaddamar makwancin da za a sanya shi, a ranar Asabar da ta gabata ne aka binne gawar tsohon shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe, a mahaifarsa ta kauyen Kutama makonni uku bayan mutuwarsa.

Iyalan marigayi Mugabe sun watsa fararen furanni a kabarin sa yayin da aka sanya gawarsa a makwancinta na karshe a kauyen da aka haife shi mai sunan Kutama wanda yake mai nisan kilomita 90 daga Harare babban birnin kasar Zimbabwe.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, an dai kammala binne gawar tsohon shugaban kasar ne a kauyensa na haihuwa Kutama bayan shafe tsawon makonni ana takaddama tsakanin gwamnatin kasar da iyalansa kan inda makwacinsa na karshe zai kasance.

Marigayi Mugabe wanda ajali ya katsewa hanzari tun a farkon watan Satumba bayan ya sha fama da rashin lafiya ta cutar daji wadda ta daina jin kowane nau'in magani, an gudanar da jana'izar sa a wani dan takaitaccen biki wanda bai samu halartar tururuwa ta jama'a ba.

KARANTA KUMA: An kashe dogarin sarkin Saudiya a Jeddah

Kafar watsa labarai ta CNN ta ruwaito cewa, a Alhamis da ta gabata ne iyalan marigayi Mugabe suka samu nasarar sasanci inda gwamnatin kasar ta ba su izinin binne gawarsa a kauyen da aka haife shi wato Kutama, sabanin inda aka saba binne gwarazan kasar da gwamnatin tayi nufi domin girmamawa.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar 6 ga watan Sataumba ne Mugabe ya yi kacibus da ajali a gadon wani asibitin kasar Singapore yana mai shekaru 95 a duniya, kimanin shekaru biyu kenan bayan da wani juyin mulki na dakarun tsaro ya kawo karshen jagorancinsa na tsawon shekaru 37.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel