Lokuta 6 da Buhari ya ki yiwa umarnin kotu da'a

Lokuta 6 da Buhari ya ki yiwa umarnin kotu da'a

A wani rahoto da jaridar The Punch ta wallafa a ranar Lahadi, 29 ga watan Satumban 2019, hawa kujerar naƙi da hukumar tsaro DSS tayi a kan sakin Omoyele Sowore, ya zamto daya daga cikin jerin lokuta da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ƙi yiwa umarnin kotu da'a.

Daga tsare mutane ba tare da hakki ba zuwa ƙin yi wa umarnin kotu biyayya, ga jerin wasu lokuta shida da gwamnatin Buhari ta tafka kura-kurai.

1. Omoyele Sowore

Omoyele Sowore wanda ya kasance tsohon takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar AAC kuma babban mawallafin kamfanin jaridar Sahara Reporters, ya shiga hannun hukumar DSS tun a ranar 3 ga watan Agustan 2019.

Hukumar DSS na ci gaba da tunumar Sowore da laifukan cin amanar kasa da laifuka na almundahanar kudade kamar yadda Muryar Duniya ta ruwaito.

A farkon makon da ya gabata ne wata babbar kotun tarayya da ke birnin Abuja, ta bai wa hukumar DSS umarnin sakin Sowore, madugun 'yan gwagwarmayar juyin juya hali na RevolutionNow. Kawo wa yanzu hukumar DSS ta yi umarnin kotun kunnen uwar shegu.

2. Ibrahim El-Zakzaky

Tun a ranar 2 ga watan Dasumban 2016, Alkali Gabriel Kolawale na babbar kotun tarayya da ke binrin Abuja, ta bayar da umarnin sakin jagoran mabiya akidar shi'a a Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaku, da kuma matarsa, Zeenatu da ke tsare a hannun hukumar DSS

Baya ga wannan umarnin da hukumar DSS ta ki girmamawa, babbar kotun ta kuma umarci hukumar da ta biya El-Zakzaky diyyar naira miliyan 50 wanda ke tsare tun a shekarar 2015 bayan wata takaddama da ta auku tsakanin mabiya Shi'a da rundunar sojin kasan Najeriya a birnin Zazzau na jihar Kaduna.

3. Sambo Dasuki

Ya zuwa yanzu tsohon mai ba da shawara kan harkokin tsaron kasa, Kanal Sambo Dasuki, ya ci gaba da bai wa duga-dugansa hutu a hannun hukumar DSS wanda ya shiga hannu tun a watan Dasumban 2015.

Baya ga umarnin kotu daban-daban a lokuta mabanbanta juna, gwamnatin shugaban kasa Buhari na ci ga da tsare Kanal Dasuki a bisa zargin sa da yn sama da fadi da kudin makamai na kimanin dala biliyan 2.1 tun a gwamnatin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Hakazalika wata kotun bunkasa tattalin arzikin kungiyar kasashen Yammacin Afirka, ta bai wa hukumar DSS umarnin sakin Kanal Dasuki a ranar 4 ga watan Oktoba na 2016, lamarin da ya zuwa yanzu hukumar ta kekashe a kai.

4. Umarnin kotu kan iyaka ta cin bashi

A ranar 20 ga watan Fabrairun 2018 ne Alkalin wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Abuja, Justice Gabriel Kolawale, ya bai gwamnatin tarayya umarnin ta sanya matuƙa ko kuma iyaka ta cin bashi a cikin kundin tsari na kudi a kasar.

Jastis Kolawale ya bai wa gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki casa'in a kan neman lamunin majalisar dattawa da kuma ta wakilai na tarayya wajen sanya matuƙa ta cin bashi, sai dai ya zuwa babu amo ballantana labarin girmama wannan umarni.

5. Kuɗaɗen da aka kwato a hannun barayin gwamnati

A watan Maris na 2016 ne Jastis Muhammad Idri na babbar kotun tarayya da ke garin Abuja, ya zartar da hukunci na umartar gwamnatin tarayya da ta wallafa yadda ta ke kashe kuɗaɗen da ta kwato a hannun wadanda suka wawure daga lalitar talakawa.

Ya zuwa yanzu gwamnatin ba ta yi wa wannan umarni da'a ba.

KARANTA KUMA: An kashe wasu yara da laifin yin bayaha a titi a kasar Indiya

6. Babban Ma'aikacin sojin ruwa, Kaftin Dada Labinjo

Har ya zuwa yanzu ana zargin cewa, Kaftin Dada Labinjo, na tsare a wani dakin turke masu laifi na karkashin kasa da ke hukumar leken asiri ta dakarun tsaro a Abuja tun a ranar 12 ga watan Satumban 2018.

Fitaccen lauya mai fafutikar kare hakkin dan Adam, Mista Femi Falana, ya ce duk da samun lamunin kotun tarayya wadda ta bayar da umarnin sakin Kaftin Labinjo, ya zuwa ya na tsare a hannun rundunar sojin rawa tare da wasu mutane kimanin 67 da suka hadar har da 'yan kasashen waje.

Cikin wata rubutacciyar da ya aike da ita zuwa ga sakataren hukumar kare hakkin dan Adam na kasa a ranar 15 ga watan Agusta, Falana ya ce Kaftin Labinji na daya daga cikin mutane 67 da rundunar sojin ruwan Najeriya ta tsare ba tare da an gurfanar da su gaban kuliya ba.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel