Bayelsa 2019: Manyan kusoshin PDP su na sauya sheka zuwa APC

Bayelsa 2019: Manyan kusoshin PDP su na sauya sheka zuwa APC

Bayan zaben fitar da gwanin da jam’iyyar PDP mai rike da jihar Bayelsa ta shirya, an samu wasu jiga-jigan jam’iyyar da su ka rika sauya-sheka bayan an ba Douye Diri tutan takarar gwamna.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, PDP ta na fama da sauyin-sheka zuwa jam’iyyar APC a sakamakon ba Sanata Douye Diri tikitin PDP a zaben gwamnan da za ayi a karshen shekarar nan.

Tuni dai babban abokin hamayyar ‘dan takarar na PDP watau Cif Ndutimi Alaibe ya garzaya kotu inda yake kalubalantar zaben da ya ba Douye Diri damar samun tsayawa PDP takara a Bayelsa.

A daidai lokacin da ake wannan rikici, ana zargin gwamna Seriake Dickson, ya na yunkurin tsaida ‘dan takarar mataimakin gwamna daga bangaren da ya fito na Yammacin Bayelsa.

Wannan zai ba gwamnan damar takarar Sanata a zabe na gaba. Sai dai kuma gwamnan zai gamu da kalubale daga bangaren tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da ke kukan ba a yi da su.

KU KARANTA: Atiku ya dumfari Kotun koli da dalilai fiye da 60 domin tunbuke Buhari

Daga cikin manyan kusoshin da su ka bar PDP bayan an yi zaben fitar da gwani akwai jigon PDP a yankin Nembe, Gabriel Jonah wanda ‘Danuwa ne wurin Mataimakin gwamna mai-ci yanzu.

Karamar hukumar Nembe ta na cikin inda APC ta ke da dinbin Mabiya. Koamwar Gabriel Jonah zuwa jam’iyyar hamayya a jihar za ta ba APC wani babban karfi a zaben Nuwamban mai zuwa.

Haka zalika a Garin na Nembe, tsohon Sanatan shiyyar kuma Aminin tsohon shugaban kasa Jonathan mai suna Nimi Brigham Amange ya tsere daga PDP inda ya koma jam’iyyar APC.

Wasu Mukarraan gwamna Seriake Dickson su na cikin wadanda su ka koma APC. Misis Helen Bob ta yi watsi da jam’iyyar PDP kamar yadda Abenego Don Evarada ta ajiye aiki ta bar PDP.

Tsohon ‘dan majalisar dokokin jihar, Parkinson Markmanuel, da Glad Stone Amabibi, da irin su Abadani Dick, Omonibeke Kemelayefa duk sun sauya-sheka daga PDP inda su ka koma APC.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel