Ba rigima ta sa Aisha Buhari ta bar Villa ba – Fadar Shugaban kasa

Ba rigima ta sa Aisha Buhari ta bar Villa ba – Fadar Shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta fito ta yi magana a game da bacewar Mai dakin shugaban kasa watau Hajiya Aisha Muhammadu Buhari wanda aka shafe watanni kusan biyu ba ta cikin kasar nan.

Kamar yadda mu ka samu labari a Ranar Asabar, 28 ga Watan Satumba 2019, fadar shugaban kasar ta yi martani a game da rahotannin da ke yawo na cewa akwai wasu sabani na cikin gida.

Fadar shugaban kasar ta karyata cewa Mai dakin Buhari ta yi nisan kiwo ne a dalilin gaza samun ta-cewa a cikin gwamnatin Buhari da kuma nuna bore kan wasu masu rike da Madafan iko.

Darektan yada labarai na ofishin Uwargidar shugaban kasar, Sulaimen Haruna, ya yi watsi da wannan surutai inda ya ce Aisha Buhari ta na da damar da za ta tafi duk inda ta ke so a Duniya.

KU KARANTA: Aisha Buhari ta yi wata da watanni ba ta Najeriya

Haruna yake cewa a matsayin Aisha Buhari na ‘yar kasa mai cikakken ‘yanci, ta na da damar zagayawa ko ina. Babban Hadimin Mai dakin shugaban kasar ya kwantar da wannan rade-radi.

Rabon da a ga Aisha Buhari tun bayan da ta bar Najeriya zuwa aikin Hajji kwanaki. Bayan kammala aikin Hajjin tare da Mai gidantan, sai su ka sheka Landan, inda har gobe ba ta dawo ba.

Rahotanni sun nuna cewa Dr. Hajo Sani ce ta ke wakiltar Mai dakin shugaban kasar a duk wani taro da aka gayyace ta. Sani babbar Mai taimakawa Matar shugaban kasar ce wajen gudanarwa.

Daga cikin taron da Aisha Buhari ta ki halarta har da wani wanda Matan shugabannnin Afrika su ka yi a Amurka. Wasu daga fadar shugaban kasar sun musanya cewa akwai wani rikici a kasa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel