Yanzu-Yanzu: An kama wani da ya yi yunkurin sace yaro daga Islamiyya a Kaduna

Yanzu-Yanzu: An kama wani da ya yi yunkurin sace yaro daga Islamiyya a Kaduna

Mazauna Makarfi Road da ke karamar hukumar Igabi na jihar Kaduna sun kama wani matashi dan shekaru 20 da suke zargi da garkuwa da mutane.

Daily Trust ta ruwaito cewa wanda ake zargin ya yi yunkurin sace wani karamin yaro ne a makarantar Iskamiyya da ke unguwar amma wasu matasa suka kama shi.

Lamarin ya faru ne misalin karfe 6 na yamma lokacin da yaran ke komawa gida bayan an tashi daga islamiyyan.

Babu cikaken bayyani kan yadda aka kama wanda ake zargin a halin yanzu amma wata 'yar unguwar da tace sunan ta Hajiya ta ce wanda ake zargin ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa inda ya ce abokin mahaifin yaron ne ya aiko shi ya kawo masa yaron.

DUBA WANNAN: Abba vs Ganduje: Kotun koli ta ki amincewa da bukatar da Ganduje ya gabatar

"Ya amsa cewa abokin mahaifin yaron ne ya turo shi ya dako yaran daga makaranta. Amma sai ya yi rashin sa'a wasu mutane da ke kusa suka kama shi. A yanzu da nake muke magana an mika shi ga jami'ar tsaro na NSCDC," inji ta.

Majiyar Legit.ng ta gano cewar an sanar da iyayen yaron kafin a mika shi caji ofishin 'yan sanda na Narayi misalin karfe 8 na dare.

Da aka tuntube shi, Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, DSP Yakubu Sabo ya ce har yanzu ba a sanar da shi afkuwar lamarin ba saboda yaka yana jiran sako daga DPO na unguwar da abin ya faru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel