Kogi: Kungiyar Miyetti Allah ta bayyana dan takarar da za ta jefa wa kuri'a

Kogi: Kungiyar Miyetti Allah ta bayyana dan takarar da za ta jefa wa kuri'a

Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), a ranar Asabar 28 ga watan Satumba ta zabi Gwamna Yahaya Bello a matsayin dan takarar gwamna da za ta jefa wa kuri'un ta a zaben jihar da ke tafe.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ta ruwaito cewa sakataren tsare-tsare na kungiyar, Alhaji Aliyu Saleh ne ya bayar da sanarwar yayin wani taron manema labarai a garin Lokoja babban birnin jihar.

Saleh ya kuma umurci 'yan kungiyar su fara abinda ya kira yakin neman zabe na 'Ruga zuwa Ruga' domin wayar da kan 'yan kungiyar su zabi Bello saboda shine ya samar musu yanayi mai kyau a jihar.

"Muna kuma goyon bayan gwamnan saboda rigafin cutar Contagious Bovine Plurol Pheneumonia (CBPP) da ya sanya aka yi wa shanun mu 23,000 a jihar kyauta," inji shi tare da yabawa gwamnan saboda daukan matakan rage rikici tsakanin makiyaya da manoma a jihar.

Saleh ya kuma ce gwamnan ya janyo su a jiki a jihar ta hanyar bawa daya daga cikinsu mukammi a gwamnatinsa tare da nada shugabanninsu cikin majalisar masu sarautun gargajiya na jihar a matakin jiha da kananan hukumomi.

DUBA WANNAN: Abba vs Ganduje: Kotun koli ta ki amincewa da bukatar da Ganduje ya gabatar

A lokacin da ya ke zantawa da manema labarai tare da shugaban MACBAN na jihar, Alhaji Umaru Jaido, Saleh ya ce 'yan kungiyar sun cimma matsayar goyon bayan takarar Bello saboda kaunar da suke yi wa Shugaba Muhammadu Buhari da jam'iyyar APC.

Kwamishinan kananan hukumomi da sarautu na jihar, Abubakar Ohere ya mika godiyarsa ga kungiyar a madadin Gwamna Bello.

Acewar Ohere, Gwamna Bello Shugabana ne mai son al'umma kuma abinda ya fi bawa fifiko a mulkinsa shine kiyaye rayukka da dukiyoyin al'umma ba tare da la'akari da kabila ko addininsu ba.

Ya kuma bayyana cewa Bello ya zabi shugabanin Fulani a kwamitin masu sarauta na jihar ne saboda a rage samun rikici tsakanin makiyaya da manoma ta hanyar fahimtar juna da tattaunawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel