Namadi Sambo ya jinjinawa El-Rufai a kan irin ayyukan da yake gudanarwa a Kaduna

Namadi Sambo ya jinjinawa El-Rufai a kan irin ayyukan da yake gudanarwa a Kaduna

Tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya, Namadi Sambo a ranar Juma’a 37 ga watan Satumba, 2019 ya jinjinawa Gwamna Nasir El-Rufai bisa kammala aikin ruwan Zaria da yayi wanda kasance tsawon shekaru 42 yana bukatar gyara.

Namadi Sambo ya bayyana farin cikinsa ne a lokacin da ya ziyarci gwamnan a fadar gwamnatin jihar Kaduna wato Sir Kashim Ibrahim House.

KU KARANTA:Kotu ta tabbatar da nasarar wani sanatan APC a jihar Kogi

Kamafanin dillacin labaran Najeriya NAN ya tattaro mana jawaban cewa aikin fadada ruwan Zaria an soma shi ne tun a lokacin da tsohon mataimakin shugaban kasan yake gwamnan Kaduna.

A yanzu haka gyaran da aka yi a kansa yana ya samar da ruwan sha ga mutane sama da miliyan biyu dake Zaria da kewaye.

“Tabbas wannan aikin na fadada gidan ruwan Zaria abin a yaba ne. Aikine wanda ya magance matsalar ruwan sha a tsakanin jama’ar garin Zaria da kewaye.

“Hakika na yi farin cikin ganin an kammala wannan aiki, kuma da ya zamo ni ne wanda soma gudanar da katafaren aiki irin wannan kana kai kuma kammala shi. Ko shakka babu hakan na nuna cewa cigaba jama’ar Kaduna shi ne abinda yafi damunka.” Inji Sambo.

Bugu da kari, tsohon mataimakin shugaban kasan ya roki Gwamnan na yayi kokarin kammala ginin asibiti mai gado 300 da gwamnatin da ta shude ta soma, inda ya ce kammala asibitin zai matukar taimakawa wurin rage matsalolin lafiya a jihar Kaduna.

Da yake martani ga tsohon mataimakin shugaban kasan, Gwamna El-Rufai ya jinjina masa a kan dora Kaduna a kan tsari da kuma taswirar zamani da ma wasu sauran ababe.

https://www.premiumtimesng.com/regional/nwest/354915-former-vp-sambo-commends-el-rufais-performance-as-kaduna-governor.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel