Kotu ta tabbatar da nasarar wani sanatan APC a jihar Kogi

Kotu ta tabbatar da nasarar wani sanatan APC a jihar Kogi

Kotun daukaka kara wadda ke zaune a babban birnin tarayya Abuja, ta tabbatar da nasarar Isah Jibrin a matsayin wanda ya lashe zaben Sanata mai wakiltar Kogi ta Gabas a zaben da ya gabata.

Kotun daukaka karar tayi watsi ne da karar Sanata Ali Atai Aidoko Usman da jam’iyyarsa ta PDP a ranar Juma’a 27 ga watan Satumba a dalilin rashin ingancin korafin.

KU KARANTA:An maka wani Farfesa kara kotu a sakamakon ya tilastawa dalibansa yin zindir a gaban aji

A lokacin da kotun ke yanke hukuncin watsi da karar tayi amfani ne da hukuncin da kotun zabe ta yanke, inda ta ce masu korafin basu da hujja ko guda daya wadda za ta iya gamsar da kotun cewa lallai Sanata Isah Jibrin ba shi bane ya lashe zabe.

Haka kuma, kotun ta kara da cewa, an gudanar da zaben ‘yan majalisar a cikin doka kamar yadda kundin tsarin zabe wato Electoral Act 2010 ya tsara. Sanata Isah Jibrin na jam’iyyar APC shi ne ya samu mafi rinjayen kuri’u don haka yayi nasara.

Sanata Jibrin ya jinjinawa kotun bisa wannan shari’a kuma ya bayyana wannan abu a matsayin yadda da aminci da mutanensa ke cigaba da ba shi tare da jam’iyyarsa ta APC.

“Wannan nasarar ba tawa ba ce ni kadai, tamu ce ni da jama’ata. Ina kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki da su zo mu hada karfi da karfe domin daga martabar Kogi ta Gabas.” Inji Isah.

A wani labarin na daban, za ku ji cewa, uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari ta kwashi tsawon watanni biyu ba ta Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tun lokacin da ta tafi Saudiya domin sauke farali a watan Agusta har yau bata dawo Najeriya ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel