Aisha Buhari ta kwashi tsawon watanni 2 ba ta Najeriya

Aisha Buhari ta kwashi tsawon watanni 2 ba ta Najeriya

Jaridar Daily Trust ta ruwaito mana labarin cewa uwargidan Shugaba Buhari wato Aisha Buhari ta kai kimanin watanni biyu yanzu ba ta Najeriya abinda ya fara janyo ce-ce kuce a fadar Villa.

Bayanan da muke samu daga majiya mabambanta na cewa uwargidan ta bar kasar ne a dalilin yin bore bisa yadda gwamnatin maigidanta ke gudanar da abubuwa a kasar.

Haka kuma Daily Trust ta tattaro mana bayanin cewa tun dai da uwargidan Shugaban kasan ta tafi kasar Saudiya a farko wata Agusta domin yin aikin hajji har yanzu ba ta dawo ba.

KU KARANTA:Kannywood: Abinda ya sa na fice daga masana'antar Kannywood – Adam A. Zango

Mahajjatan da suka tafi kasar Saudiya domin sauke farali daga nan Najeriya sun jima da dawowa gida, amma sai dai wata majiya wadda ke da kusanci da Villa ta sanar damu cewa tun bayan kammala aikin hajjin uwargidan shugaban kasan ta wuce Landan.

“Mama (wato uwargidan shugaban kasa) tana Landan. Daga Saudiya ta wuce zuwa birnin Landan,” kamar yadda wata majiyar ta fada mana.

Da kuma aka tambayi majiyar labarin dawowarta sai ta ce: “Ban sani ba, abinda kawai na sani shi ne tana Landan.” An fara lura da cewa lallai bata kasar nan kasancewar anata yin abubuwan da ya kamata a ganta a wurin amma shiru kake ji.

Bugu da kari, wakilin Daily Trust ya bamu tabbacin cewa hatta bikin babbar sallah da Shugaban kasa yayi a Dauran jihar Katsina, inda yayi ta karbar manya-manyan baki matar tasa bata nan.

Gani na karshe da aka yiwa Aisha Buhari shi ne a farkon watan Yuli da suka tarbi jakadiyar Nijar a Najeriya tare da maigidanta Shugaba Buhari a Villa.

https://www.dailytrust.com.ng/aisha-buhari-away-from-nigeria-for-2-months.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel