Tashin hankali: Miji ya kone matarshi kurmus akan rikicin sayar da fili

Tashin hankali: Miji ya kone matarshi kurmus akan rikicin sayar da fili

- An kama wani mutumi a jihar Ondo da ya kone matarsa kurmus har lahira

- An ruwaito cewa mutumin yayi hakan ne saboda rikicin da suke da matarsa akan wani fili da ya sayar

- Makwabtan mutumin sun bayyana cewa su dai kawai sun hango wuta na ci daga cikin dakin mtar ne, inda suka yi gaggawar garzayawa da ita asibiti

'Yan sanda jihar Ondo sun kama Ojo Daniyan da laifin sanyawa matarshi Dorcas wuta, saboda ta nuna rashin amincewarta kan filin shi da ya sayar.

A cewar wani wanda lamarin ya faru a gabanshi, mutumin wanda aka bayyana cewa sana'ar walda yake yi, ya zazzagewa matarshi galan na fetir a ranar Asabar dinnan da ta gabata, kafin daga bisani ya kunna mata wuta.

"A lokacin da wutar ta fara ci, wani daga cikin mu ne ya hango hayaki na fitowa daga cikin dakinsu.

"Mun yi saurin ceto ta, inda muka yi gaggawar garzayawa da ita asibiti, sai dai kuma a asibitin rai yayi halin shi," in ji wanda lamarin ya faru a gaban shi.

Da yake tabbatar da kama wanda ake zargin, kakakin rundunar 'yan sandan Femi Joseph, ya ce da sun gama gabatar da bincike a kan mai laifin za su tura shi kotu domin gabatar da bincike akan shi.

KU KARANTA: Dalla-dalla yadda na rabar da miliyan dari hudu da Dasuki ya bani - Olisa Metuh ya tona asiri

Ga abinda kakakin rundunar 'yan sandan ya ce: "Duk da dai shi wanda ake tuhumar ya musanta zargin da ake yi masa, amma mun san cewa tabbas yafi kowa sanin abinda yake fada mana.

"Misali, 'yarsu ta sanar da mu cewa mahaifinsu ya siyo fetur a cikin galan ya ce kowa ya fita daga dakin da suke zaune.

"Amma sai mahaifiyarmu taki fita da misalin karfe 11 na dare, sai suka fara ganin wuta ta kama a dakin da take baccin.

"Kafin su farga har ta kone kurmus. Yanzu haka dai muna gabatar da bincike akan lamarin kuma zamu kawo karshen shi," in ji kakakin rundunar 'yan sandan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel