Wata sabuwa: Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sauke shugaban kotun IST

Wata sabuwa: Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sauke shugaban kotun IST

- Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sauke shugaban kotun sauraron kararrakkin tsaro da hannayen jari

- Har yanzu dai ba a gano dalilin saukesa ba duk da ma'aikatan kotun dai sun turawa EFCC bukatar bincikar shugaban

- An maye gurbinsa da Jude Udunni, wanda shine babban ma'aikaci a bayan Idoko

A ranar Alhamis ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta sauke shugaban kotun sauraron kararrakin tsaro na hannayen jari (IST), Isiaka Idoko, daga ofishinsa.

Har yanzu dai gwamnatin tarayya bata sanar da dalilin saukesa ba.

Idoko lauya ne daga jihar Kogi ya yi aiki da hukumar SEC ta Najeriya kafin ya yi murabus a 2006 a matsayin darakta.

KU KARANTA: Jirgin-kwantar-da-tarzoma-ya-yi-hatsari-a-jamhuriya-afirka-ta-tsakiya

Har yanzu dai ba mu san ko dalilin zargin rashawa da kungiyar ma'aikatan ke masa ne yasa aka saukesa.

IST ma'aikatar shari'a ce mai zaman kanta wacce aka kirkiro karkashin sashi na 224 na dokokin tsaro a 1999.

Jaridar Premium Times ta gano cewa, majiya mai karfi daga kotun sauraron kararrakin tsaro da hannayen jarin ta gano cewa Jude Udunni, ne zai maye gurbinsa.

Fusatattun ma'aikatan kotun ne suka mika kara ga EFCC akan zargin rashawa da suke was Idoko.

Kwamitin da aka sa bincike akan zargin basu samo komai ba.

Amma kuma wasikar da babban sakataren tarayya na ma'aikatar kudi, Mahmoud Isa Dutse, yasa hannu, ta umarci Idoko da ya mika shugabanci ga babban ma'akacin kotun sauraron kararrakin baya da shi.

An zabi shugaban ne a 2017 tare da wasu mutane 9 bayan da kotun sauraron kararrakin tsaroda hannayen jarin ta yi shekaru biyu bata aiki.

Kotun na da kwararren sani akan kasuwanci, tsaro da dokokin fansho sakamakon kwarewa ma'aikatanta..

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel