'Yan sanda sun kama wanda ya kashe mata da mijinta da diyarsu a Kano

'Yan sanda sun kama wanda ya kashe mata da mijinta da diyarsu a Kano

Rundunar 'Yan sandan na jihar Kano a daren Juma'a ta tabbatar da kama wani Salisu Idris dan shekaru 25 da aka ce ya bankawa wani gida wuta inda ya yi sanadin mutuwar mutane uku 'yan gidan.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da kama wanda ake zargin inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba da ta gabata a kauyen Gayawa Tsohuwa a karamar hukumar Ungogo na jihar inda ma'auratu biyu da diyarsu mace daya ta mutu.

Ya ce, "A ranar Laraba, misalin 3 na dare mun samu rahoton gobara mai daure kai a Gayawa Tsohuwa da ke karamar hukumar Ungogo da mu kayi alkawarin bincike. Bayan rahoton, kwamishinan 'yan sanda ya kira dukkan jami'an sashin binciken kwakwaf ciki har da DPO na Zango ya basu awa 254 domin su nemo wadanda suka aikata wannan mummunan aiki wadda hakan yasa suka bazama suka fara bincike.

"Ta hanyar amfani da wasu dabarun mu mun kama wani Salisu Idris mazaunin kauyen Gayawa Gabas a karamar hukumar Ungogo. Mun binciko inda ya ke kuma mun samu rauni na kunan wuta a jikinsa. Bayan mun masa tambayoyi mun gano cewa su biyu suka aikata mummunan aikin. Daya har yanzu bai shigo hannu ba amma zamu kamo shi."

DUBA WANNAN: Harin da aka kaiwa Pantami: 'Yan sanda sun gayyaci jiga-jigan PDP 3 don amsa tambayoyi

Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai, wanda ake zargin ya amsa aikata laifin inda ya ce an dauki hayansa ne ya kona gidan inda akayi masa alkawarin N200,000.

Idris, wanda ke sana'ar sayar da waya a Farm Centre ya ce yana son ya yi amfani da kudin ne ya shiga Jami'ar Yusuf Maitama Sule na Kano.

Ya ce, "Wani aboki na ya ce in raka shi gidan kuma ya yi alkawarin zai bani N200,000 indan mun gama. Mun isa gidan kamar karfe 2 na dare muka haura katanga dauke da man fetur kuma muka kyasta ashana, garin haka na kone a hannu da kafa na.

"Ban fadawa kaka na gaskiya abinda ya faru ba, na fada masa cewa a wurin mai shayi na kone."

A cewar Idris, an garzaya da shi zuwa asibitin garinsu daga bisani aka tura shi wani asibiti a Minjibir inda 'yan sanda suka gano shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel