Dalilin da yasa na siyar da 'ya'yana uku a N500,000, in ji wata mata

Dalilin da yasa na siyar da 'ya'yana uku a N500,000, in ji wata mata

- Jami'an tsaro sun kama kungiyar safarar kananan yara a jihar Legas

- A cikinsu har da matar da ta siyar da yaran cikinta har 3 akan N500,000

- Ta bayyanawa jami'an tsaro cewa tsananin rayuwa ne da rashi suka tasa ta gaba

Blessing Stephen mai shekaru 25 da bayyana dalilin da yasa ta siyar da 'ya'yanta uku akan N500,000.

Jami'an tsaro sun cafke Stephen wacce suke zargi da zama 'yar wata kungiyar safarar yara kanana.

Sauran 'yan kungiyar da aka kama sun hada da: Una Godwin mai shekaru 58, Blessing John mai shekaru 27, Israel Ariyo mai shekaru 33, Itoro Anthony mai shekaru 40 da Mforbong Ntoro mai shekaru 48.

Jami'an tsaron sun bazama Neman daya daga cikin wadanda aka zargin, John, wanda ya yada yaro mai watanni hudu a duniya a wata majami'a da ke yankin Ketu na jihar Legas.

An zargi cewa John ya sace yaro a Ikota Housing Estate a watan Yuli inda ya siyar da shi a jihar Akwa Ibom a N350,000.

KU KARANTA: Ke-duniya-yaro-mai-shekaru-7-a-duniya-da-fashi-da-makami

City Round ta gano cewa makwaftan Ntoro, wacce aka siyarwa jaririn sun fara zarginta sakamakon kukan yaron. Hakan kuwa yasa ta maidawa John yaron tare da bukatar bata wani a maimakonsa.

An gano cewa, John ya maida jinjirin Legas inda ya yadda yaron a kusa da cocin.

Manema labarai sun gano cewa, hukumar majami'ar sun kaiwa 'yan sandan yankin Ketu kara inda daga baya aka gano iyayen yaron.

Jami'an tsaro sun binciko wadanda ake zargin ne ta hanyar bibiyar sahun John. Bayan kamasa sai yace akwai abokan aikinsa, Stephen da Ntoro.

Stephen ta sanar da jami'an tsaron cewa tsananin rayuwa ce ta sanyata fadawa safarar kananan yara. Ta kara da cewa tana bukatar kudi ne don magance cutar da ke damunta.

Ta kara da cewa ta siyar da yaranta uku ga Ntoro wacce ke siyar da yaran ga mutane daban-daban.

Ta ce, "Ina zama a Ikota, Ajah. Na yi soyayya da wani Julius Abang kuma ya yi min ciki. A 2010 na haifa yaron Namiji amma tsananin rayuwa ta sa na siyar da shi N150,000 ga Ntoro wacce ta shawarceni da yin hakan,"

"Na kara haihuwa da wani matukin babban mota. Shima na haifa yaro namiji inda na siyar dashi N100,000," In ji ta

"A 2013 na hadu da wani dan achaba inda na samu ciki. Rashin kudi yasa bayan na haihu muka siyar da yaron N250,000. Bayan nan ne Ntoro ta kirani daga kauye cewar tana bukatar jinjiri. A nan ne aka kamamu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel