Kaico: Mata da miji sun sayar da diyansu 2 a kan N350,000

Kaico: Mata da miji sun sayar da diyansu 2 a kan N350,000

Tawagar jami’ai masu hazaka na ‘yan sanda dake karkashin ofishin Sufeto janar sun bankado wasu wuraren da ake sayar da yara kanana a kudancin Najeriya. Jihohin kuwa sun hada da Oyo, Legas da Akwa Ibom.

Daga cikin mutanen da aka kama da aikata wannan laifi akwai wata mata mai suna Blessing Steven da mijinta Israel Ariyo wadanda suka sayar da diyansu biyu a kan kudi naira 350,000 kacal.

KU KARANTA:'Yan bindiga sun sace manyan jami'an NSCDC biyu a jihar Edo

Majiyar Vanguard ta tattaro mana bayanan cewa, mutum shida jami’an ‘yan sanda suka samu nasarar damkewa. Ga sunayen mutanen kamar haka; Blessing John, Itoro Anthony, Una Ekong, Mforbong Itoro, Blessing Steven da mijinta Israel Ariyo.

A watan Yulin 2019 ne tawagar jami’an ‘yan sandan ta kama Blessing John a lokacin da aka wani yaro dan shekaru hudu da niyyar a kais hi Akwa Ibom a sayar kan kudi N350,000.

Wannan yaron da aka sace, mai suna Ojo Ifapounda ya cigaba da ihu yana kwarara kuka a sakamakon halin da ya tsinci kansa a ciki. Su kuwa iyayen yaron tuni suka rubuta wasika zuwa ga Sufeto janar na ‘yan sanda ake satar wannan yaro na su.

Bayan da wannan wasika ta isa hannun Sufeto janar Mohammed Adamu nan da nan ya tashi tawagar IRT a karkashin jagorancin DCP Abba Kyari inda suka dira jihar Legas suka shiga bincike har Allah Ya basu sa’ar kama wadannan mutane 6.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel