Dalla-dalla yadda na rabar da miliyan dari hudu da Dasuki ya bani - Olisa Metuh ya tona asiri

Dalla-dalla yadda na rabar da miliyan dari hudu da Dasuki ya bani - Olisa Metuh ya tona asiri

- Tsohon sakarataren jam'iyyar PDP da ake shari'arsa a kotu dangane da wasu makudan kudade da ya cinye, ya bayyana wani sirri

- Olisah Metuh ya bayyana yadda ya rabar da naira miliyan dari hudu da Sambo Dasuki ya bashi

- Metuh dai hukumar EFCC ce ta gurfanar da shi a gaban kotu da laifuffuka har guda bakwai

A jiya Juma'a ne 27 ga watan Satumba tsohon sakataren jam'iyyar PDP na kasa, Olisah Metuh, ya bayyanawa babbar kotun tarayya dake Abuja, wacce mai shari'a Okon Abang yake jagoranta, yadda ya rabar da miliyan dari hudu (N400m) da ya karba a wajen tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a harkar tsaro, Sambo Dasuki.

Tsohon sakataren dai hukumar yaki da cin hanci da rashawa na tuhumar sa da kuma kamfaninsa mai suna Destra Investment da laifin fitar da kudi har naira miliyan dari hudu ta hanyar da bata dace ba.

Bayan hukumar ta bayyana asusun shi a lokacin da yake da naira miliyan shida da digo shida, kafin ya samu shigowar naira miliyan dari hudun a ranar 24 ga watan Nuwambar shekarar 2014, Metuh ya yiwa kotu bayanin yadda ya rabar da wannan makudan kudade, wanda ya bayyana cewa an yiwa kasa aiki da su.

KU KARANTA: Wa'iyazubillah: An kama uba dumu-dumu yana zina da diyarshi ta cikinsa

Metuh ya ce akwai kudi kimanin naira miliyan 7.5 da aka biya kamfanin CNC a ranar 2 ga watan Disamba, da kuma naira miliyan 21.7 da aka turawa Cif Anenih sannan kuma da naira miliyan 50 da aka turawa Kanay/Olisah Metuh wanda suke da asusu guda daya a ranar 4 ga watan Disambar 2014. A ranar dai kuma ya kara bayyana cewa an turawa Richard Ehidioha naira miliyan 31.5.

Haka kuma ya sake sanar da kotu yadda aka biya kamfanin Daniel Ford International naira miliyan 200 da kuma miliyan 300 duka a ranar 4 ga watan Disambar.

Ya zuwa yanzu dai alkalin kotun ya daga sauraron karar har zuwa ranar 30 ga watan Satumbar nan, inda za a zauna a cigaba da sauraron karar ta shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel