Harin da aka kaiwa Pantami: 'Yan sanda sun gayyaci jiga-jigan PDP 3 don amsa tambayoyi

Harin da aka kaiwa Pantami: 'Yan sanda sun gayyaci jiga-jigan PDP 3 don amsa tambayoyi

- Rundunar 'yan sanda ta fara bincike kan harin da wasu da ake zargin 'yan Kwankwasiyya ne suka kaiwa Ministan Sadarwa, Dakta Isa Ali Pantami a filin tashin jiragen sama

- Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Kano ya ce an gayyaci wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP na Kano ciki har da shugaban jam'iyyar Alhaji Rabiu S. Bichi

- Rundunar 'yan sandan ta ce ba a kama kowa ba a halin yanzu amma ana cigaba da bincike domin gano wadanda suka kai harin

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta sanar da cewa ta gayyaci wasu jami'an jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, kan zargin harin da akayi ikirarin cewa wasu matasa 'yan 'Kwankwasiyya ne suka kai wa Ministan Sadarwa, Dakta Isa Ali Pantami a filin tashin jiragen Kano na Aminu Kano a farkon makon nan.

A yayin da ya ke zantawa da manema labarai a ranar Juma'a, mai magana da yawun rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce an gayyaci wasu jami'an jam'iyyar saboda binciken da ake yi don gano ainihin wadanda suka kai harin kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Abba vs Ganduje: Kotun koli ta ki amincewa da bukatar da Ganduje ya gabatar

Mista Kiyawa ya ce, "Gaskiya ne mun gayyaci wasu jiga-jigan PDP ciki har da shugaban jam'iyyar, Alhaji Rabi'u S. Bichi, Direktan yakin neman zaben PDP a zaben 2019, Dakta Y.A. GDangoni da dan mataimakin gwamna, Aminu Abdulsalam. Mun gayyace su zuwa ofishin Kwamishinan 'yan sanda, Ahmed Iliyasa kuma shugaban DSS ya hallarci zaman."

A cewarsa, ana nan ana cigaba da gudanar da bincike kuma ba a kama kowa ba.

Da ya ke tsokaci kan lamarin, Malam Sanusi Bature Dawakintofa, mai magana da yawun dan takarar gwamnan PDP a zaben da ta gabata, Abba K. Yusuf, ya ce wadanda ke tsaron ministan ne ba su yi aikinsu yadda ya dace ba.

Ya ce ba kungiyar Kwankwasiyya ba ce ta kai harin domin jagoran tafiyar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gargadi mambobin kungiyar su kasance masu biyaya ga doka a yayin da za su tafi bankwana da 'yan uwansu da za su tafi kasashen turai domin yin karatu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel