'Yan bindiga sun sace manyan jami'an NSCDC biyu a jihar Edo

'Yan bindiga sun sace manyan jami'an NSCDC biyu a jihar Edo

'Yan bindigan sun sace jami'an hukumar tsaro ta NSCDC biyu a hanyarsu ta zuwa Benin daga arewacin jihar Edo kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Lamarin na faruwa ne kwanaki uku bayan masu garkuwa da mutane sun sace matar shugaban hukumar kula da jiragen kasa na jihar.

An sace Francins Okunwe, wanda shine kwamandan NSCDC na Edo ta Arewa kuma DPO na Irrua da kuma babban sufritanda na hukumar Albert Eguavoen a Ewosaa kafin karamar hukumar Igueben a jihar misalin karfe 2 na rana.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Danmallam Mohammed ya tabbatar da afkuwar lamarin kuma ya ce 'yan sanda suna bin sahum miyagun domin ceto wadanda aka sace.

DUBA WANNAN: Abba vs Ganduje: Kotun koli ta ki amincewa da bukatar da Ganduje ya gabatar

An gano cewa jami'an tsaron su bi ta hanyar Igueben ne saboda rashin kyawun titin Benin-Auchi-Okenne.

Wata majiya ta ce, "An gano motar da suke tafiya ciki kirar Toyota Sienna a inda aka yar da shi yayin da an aike da wasu jami'an NSCDC zuwa wurin.

"Suna hanyarsu ta zuwa Benin ne amma saboda rashin kyawun hanyar Auchi-Benin-Okenne, sun canja hanya zuwa Igueben domin kaucewa hanyar mara kyau. Amma kuma sai lamarin ya faru kusa da Ewossa kafin Ekpon."

Mai magana da yawun rundunar na jihar, Efosa Ogbebor bai tabbatar da afkuwar lamarin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel