Dalilin da yasa jami'ar Bayero da ke Kano ta kori dalibai 63 tare da dakatar da 13 na shekara daya

Dalilin da yasa jami'ar Bayero da ke Kano ta kori dalibai 63 tare da dakatar da 13 na shekara daya

- A ranar juma'a ne manem labarai suka samu sanarwar korar dalibai 63 da dakatar da 13 na shekara daya da jami'ar Bayero ta yi

- Hakan na kunshe a takardar da daraktar jarabawa ta makarantar, Amina Umar Abdullahi ta sa hannu kuma ta ba manema labarai

- Ta ce hakan ya biyo bayan bukatar kwamitin ladabtarwar makarantar ne da majalisar zartarwa ta amince da shi

Shugaban jami'ar Bayero da ke Kano, Farfesa Muhammad Yahuza, ya kori dalibai 63 tare da dakatar da dalibai 13 na shekara daya sakamakon kamasu da aka yi da laifin satar jarabawa.

Wannan na kunshe ne a takardar da daraktan jarabawa na makarantar, Amina Umar Abdullahi ta sa hannu tare da baiwa manema labarai a Kano ranar juma'a.

KU KARANTA: Abun-kunya-saurayi-ya-yi-satar-wayoyi-da-jaka-a-gidan-sirikai

Kamar yadda ta ce, an dau matakin ne sakamakon bukatar hakan da majalisar zartarwar makarantar ta gabatar akan hukuncin satar jarabawa.

Kwamitin ladaftarwa na majalisar zartarwar ya gabatar da bukatar ne a taro majalisar na 374 wanda aka yi a ranar 28 ga watan Agusta, 2019.

Ta ce daliban da aka kora sun hada da dalibai goma wadanda ba digirin farko suke ba, 10 daga makarantar cigaba da karatu, 7 daga sashin kimiyyar kiwon lafiya da kuma 7 daga sashin kimiyyar na'ura mai kwakwalwa.

"Hakazalika, akwai 6 daga cikin dalibai masu karantar koyarwa da malumta, 6 daga sashin karatun engineering da sauransu," ta kara da cewa.

"Sashin karatun addinin musulunci da zane-zane na da dalibai bibbiyu. Sashin karatun sadarwa da sashin karatun jinya na da dalibai dai-daya." In ji ta.

Ta ce, majalisar zartarwar makarantar ta bukaci a baiwa dalibai 19 wasikar Jan kunne sakamakon laifukansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel