Mai garkuwa da mutane ya fadi dalilin da yasa ya ke kashe wadanda ya sace bayan an biya shi kudin fansa

Mai garkuwa da mutane ya fadi dalilin da yasa ya ke kashe wadanda ya sace bayan an biya shi kudin fansa

- Iorwuese Ikpila ya ce ya kashe mutane 16

- A cewar gawurtaccen mai garkuwa da mutanen, yana amfani da jinin wadanda ya kashe ne domin tsafi

- Ikpila ya yi ikirarin cewa an umurci ya bawa dodo jinin mutane 20 da ya kashe

Iorwuese Ikpila da aka fi sani da Dakta Kwagh Akorom Me Nenge (Ka kama ni idan za ka iya) wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane da 'yan sanda suka kama cikin 'yan kwanakin nan ya ce ya kan kashe wadanda ya sace ko bayan an biya shi kudin fansa.

Hatsabibin ya yi ikirarin cewa ya kashe mutane 16 kuma ya yi amfani da jininsu wurin tsafi domin ya samu arziki da mulki.

A cewarsa, an umurci ya kashe mutum 20 ya yi tsafi da jininsu.

Ya ce, "Daga nan ni da mutane na mu kan sace mutane ku kashe su mu bawa 'Sarauniyar' mu jininsu domin mu samu arziki da mulki.

DUBA WANNAN: Abba vs Ganduje: Kotun koli ta ki amincewa da bukatar da Ganduje ya gabatar

"Na fara wannan harkar watanni uku da suka shude saboda 'Sarauniya' ta ce mu cikashe adadin mutane 20 domin mu samu dukkan abinda muke so amma kawo yanzu mutane 16 muka kashe."

Ikpila ya shaidawa jami'an tsaro dalla-dalla yadda ya ke kashe wadanda ya sace. Sai dai yanzu ya ce ya fahimci Allah ne mai dukkan mulki kuma shine mabuwayi.

"Bayan mun kashe wadanda muka sace, mu kan sace kayansu, mu shage su sai mu bawa 'Saurauniyar' mu jininsu sannan mu binne su.

"Amma yanzu na gano cewa Allah shine mabuwayi. Kafin yanzu na fadawa 'yan sanda dukkan zunuban da nayi. Ya kuma kai ni wurin fasto tun kafin in nuna masa kaburburan wadanda muka kashe nan ma na nemi afuwa," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel