Kotun koli ta tabbatar da nasarar wani dan majalisar tarayya

Kotun koli ta tabbatar da nasarar wani dan majalisar tarayya

- Kotun koli ta tabbatar da nasara Chike Okafor a zaben majalisar wakilai da ya gabata

- Uzoma Mary-Ann ce ta daukaka karar zuwa kotun kolin sakamakon kalubalantar hukuncin shari'ar kotun daukaka kara

- Hakan kuwa ya tabbatar da dan majalisar a matsayin sahihin wakilin mazabar Ehime Mbano/Ihitte Uboma/Obowo ta jihar Imo

A ranar Alhamis kotun koli ta kori daukaka karar Uzoma Mary-Ann ta hannun lauyanta Mohammed Ndariani Mohammed wacce ke kalubalantar nasarar Chike Okafor a kotun daukaka kara.

Hakan ya tabbatar da dan majalisar a matsayin sahihin wakilin Ehime Mbano/Ihitte Uboma/Obowo na jihar Imo.

Mai kalubalantar shariar , Uzoma Mary-Ann ta daukaka kara ne ta hannun lauyanta Mohammed Ndariani Mohammy a ranar 16 ga watan Augusta don kara duban hukuncin mai shari'a Kawo Bello na kotun daukaka kara da ke Kubwa, Abuja.

KU KARANTA: Abun-kunya-saurayi-ya-yi-satar-wayoyi-da-jaka-a-gidan-sirikai

Da shi da lauyan mutum na uku, karamin ministan ilimi da tsohon dan majalisa, Chukwuemeka Nwajiuba da Farfesa Hakeem Olaniyan sun kalubalanci daukaka karar tare da rokon kotun kolin da ta yi adalci ta hanyar kara duba hukuncin kotun daukaka karar wanda hakan ne ya tabbatar da Okafor a kujerarsa.

Amma Solomon Umoh, lauyan Chike Okafor da Babatunde Kwame Ogala da jam'iyyar APC sun kalubalanci hukuncin farko na kotun daukaka karar.

Masu shari'ar biyar na kotun kolin da suka saurari shari'ar su ne: mai shari'a Olabode Rhode Vivour, mai shari'ar Chima Centus Nweze, mai shari'a Aminu Sanusi; mai shari'a Ejembi Eko, mai shari'a Uwani Musa Abba Aji.

Sun amince da kalubalen tare da watsi da hukuncin kotun daukaka karar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel