Gwamnatin jihar Benue ta bayyana sunayen mutane 11 da aka samu kaburburansu a wani kauye

Gwamnatin jihar Benue ta bayyana sunayen mutane 11 da aka samu kaburburansu a wani kauye

- A cikin kwanakin nan ne 'yan sandan jihar Benue suka gano kaburbura 11 a kauyen Gbatse na karamar hukumar Ushongo ta jihar

- Ana zargin masu garkuwa da mutanen yankin da birne mutanen da basu biya kudin fansa ba ko kuma suka musu fashi

- An gano sunayen mutanen da aka birne din ne bayan da jami'an tsaro suka cafke shugaban kungiyoyin masu garkuwa da mutanen da 'yan fashin

'Yan sandan jihar Benue sun gano kaburbura 11 a kauyen Gbatse a karamar hukumar Ushongo inda ake zargin masu garkuwa da mutane sun birne wadanda suka kashe.

Jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan jihar, ASP Catherine Anene, ya sanar da manema labarai a Makurdi cewa an kama daya daga cikin wadanda ake zargi, "Ana kammala bincikarsa za a bada cikakken bayani".

An gano cewa, wanda ake zargin, shugaban kungiyar masu garkuwa da mutane ne da kuma 'yan fashi da makami. An kamasa ne sakamakon bibiyarsa da mutanen yankin suka dinga.

KU KARANTA: Mahaifinta-ya-sanya-ta-a-mari-tare-da-garkameta-na-shekaru-2-saboda-auren-dole

Ana zargin kungiyar ta sa da fashin babura da kashe mutanen tare da birnesu don boye laifinsu don gudun hukuncin hukuma.

Shugaban kungiyoyin, Iorwuese Kpila, wanda aka fi sani da Dr. Kwagh Akoronmenenge, an kamasa ne tare da wasu mutane 6 'yan kungiyar.

Kamar yadda 'yan sandan suka fada, maboyar Kpila na nan a saman tsauni zagaye da wasu gidajen gargajiya da wajen bautar addinin gargajiya.

A inda lamarin ya faru, Gwamna Samuel Ortom ya ce, "Zamu gano tushen garkuwa da mutane a jihar nan. Zamu ganosu kuma zasu fuskanci hukuma. Duk masu garkuwa da mutane a kananan hukumomin Vandeikya, Logo, Ukum, Kwande da Katsina-Ala zamu bincikosu. Gwamnatina bazata mika wuya ga 'yan ta'adda ba."

Shugaban karamar hukumar, Bemsen Agugu, ya bada sunayen mutanen da aka birne kamar haka: Aondowase Akaa-har; karamar hukumar Terlum, Tema-Shangev-Ya; karamar hukumar Kwande, Ushahemba Ulughf daga karamar hukumar Mbakyaa, Shangev-ya daga karamar hukumar Kwande, Avakaa Adema daga karamar hukumar Tse Akanyi-Mbarumun, Nanev daga karamar hukumar Kwande, Tughgba Akosu daga karamar hukumar kwande, Ushahemba Adasu daga karamar hukumar Vandeikya da Aondohemba Kunav da ke kusa da babban asibitin Vandeikya.

Wadanda aka kama kamar yadda shugaban ya sanar sune: Iorwuese Kpila wanda aka fi sank da Dr Kwagh akorom menenge, Tersoo Agee Agabi Charles, Ortema wanda aka fi sani da ten tyres da Chiahemba Baa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel