Abba vs Ganduje: Kotun koli ta ki amincewa da bukatar da Ganduje ya gabatar

Abba vs Ganduje: Kotun koli ta ki amincewa da bukatar da Ganduje ya gabatar

Kotun koli a ranar Juma'a tayi watsi da bukatar da Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano, INEC da jam'iyyar APC suka gabatar ne kallubalantar daukaka kara da PDP da dan takarar ta Abba Yusuf su kayi na gabatar da wasu shaidu a kotun sauraron zabe.

Lauyoyin biyar karkashin jagorancin Mary Odili sun amince da hukuncin na kotun daukaka kara na umurtan kotun zaben ta bawa PDP damar gabatar da wasu shaidu da kotun ta ki sauraron shaidansu a baya kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

A ranar 29 ga watan Yuli, kotun daukaka kara da ke Kaduna ta amince da bukatar PDP da dan takarar gwamnan ta, Abba Yusuf ne neman a bari su gabatar da wasu shaidu a gaban kotun zabe.

An shigar da karar ne bayan kotun sauraron karrakin zabe na Kano a ranar 16 ga watan Yuli ta haramtawa wasu shaidun PDP takwas masu muhimmanci su gurfana gaban ta domin bayar da shaida.

DUBA WANNAN: Wani dan kasuwa ya sheka barzahu bayan kammala 'sukuwa' da budurwarsa a otel

Sunayen shaidun takwas sun hada shugaban PDP na karamar hukumar Bichi, Umar Tanko wadda ya yi ikirarin cewa a gabansa aka yi badakallar kwace sakamakon zaben mazabar Gama duk da cewa an gabatar da rubutaccen shaidunsu a gaban kotun tunda farko.

A ranar 18 ga watan Satumba ne wadanda aka yi kara - INEC, APC da gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje suka kamalla gabatar da hujojjinsu a rubuce.

Shugaban alkalan kotun zaben, Halima Shamaki ta ce kotun na sace da adadin kwanaki 180 da dokar zabe ta bashi domin yanke hukunci hakan yasa suke kokarin kammala aikinsu domin su yanke hukunci kafin cikar wa'adin.

Bayan bangarorin biyun sun kammala gabatar da hujjojinsu, Mai shari'a Shamaki ta jinkirta yanke hukunci ba tare da fadin rana ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel