Kotu ta bayar da umurnin kwace kudin da aka alakanta da Oyo-Ita

Kotu ta bayar da umurnin kwace kudin da aka alakanta da Oyo-Ita

Wata babban kotun tarayya dake Abuja ta bada unurnin karbe wasu kudaden da wani mai alaka da Shugaban Ma’aikatan Tarayya Winifred Oyo-Ita, ya dawo da dasu.

An tattaro cewa mai shari’an, Folashade Ogunbanjo-Giwa ta bayar da umurnin mallakawa gwamnatin Najeriya kudaden a ranar Alhamis, 26 ga watan Satumba.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 18 ga watan Satumba, ya dakatar da Misis Oyo-Ita domin ba hukumar yaki da cin hanci da rashawa damar kammala bincikenta. Hukumar EFCC ta zarge ta da aikata rashawa.

A lokacin zaman kotu a ranar Alhamis, wani lauyan hukumar, M.A Abubakar ya gabatar da wani bukata sannan ya kuma bayyana cewa an dawo wa da hukumar kudin ne ba tare da wahala ba.

Mista Abubakar ya tunatar da kotun game da umurnin farko da tayi a ranar 28 ga watan Yuni, wanda ya amince da kwace kadarorin na wucin gadi.

KU KARANTA KUMA: El-Rufai ya yi ba’a ga Shehu Sani, yace bai cancanci a dauke shi aiki a ma’aikatun gwamnatin jihar ba

Ya fada ma kotun cewa a halin da ake ciki a ranar Alhamis babu wanda ya gabatar da kara don kalubalantan wannan umurni na kwace kadadorin.

Yayin da yake bukatan mai shari’ar ta bada umurnin kwace kaddarorin na dindindin, Mista Abubakar ya sanar da kotun cewa an biya kudin ne zuwa asusun bbabban bankin Najeriya bayan mai laifin ya dawo da kudaden.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel