El-Rufai ya yi ba’a ga Shehu Sani, yace bai cancanci a dauke shi aiki a ma’aikatun gwamnatin jihar ba

El-Rufai ya yi ba’a ga Shehu Sani, yace bai cancanci a dauke shi aiki a ma’aikatun gwamnatin jihar ba

- Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna yayi ba’a ga tsohon Sanata Shehu Sani, cewa bai da tabbacin ko ana iya daukar dan majalisar aiki a ma’aikatun gwamnatin jihar

- Hakan na zuwa ne bayan wani mai amfani da shafin Twitter, Safiu Kajuru, ya bukaci El-Rufai da ya fara biyan sanatan mafi karancin albashi domin ya siya hankali

- A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shehu Sani yayi martani a kan sanya Abubakar makarantar gwamnati da Gwamna Nasir El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa bai da tabbacin ko Sanata Shehu Sani ya cancanci a dauke shi aiki a ma’aikatun gwamnatin jihar.

Furucin El-Rufai martani ne ga bukatar wani mai amfani da shafin Twitter, Safiu Kajuru, da ya nemi a fara biyan taohon sanatan mafi karancin albashi domin yayi amfani dashi wajen siyawa kansa hankali.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisa ta takawas, Shehu Sani yayi martani a kan sanya Abubakar makarantar gwamnati da Gwamna Nasir El-Rufai.

Sani ya ce gwamnan yayi amfani ne da salon yaudara a siyasance domin yaudarar al’ummomin dake wajen Kaduna kasancewar ba su san yadda makarantun gwamnatin jihar suka lalace ba.

KU KARANTA KUMA: Zargin zamba: A shirye nake na fuskanci Osinbajo a kotu – Timi Frank

Ya kuma bayyana wannan aiki a matsayin wasan kwaikwayon Kannywood ko kuma Nollywood, ba komi ya sanya shi wannan abu ba, banda zabe mai zuwa na 2023.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel