An kashe dan kwallon Najeriya, Junior Duru yayin harbe-harbe da wasu kungiyoyin asiri su kayi

An kashe dan kwallon Najeriya, Junior Duru yayin harbe-harbe da wasu kungiyoyin asiri su kayi

An kashe fitaccen dan kwallon Najeriya, Junior Duru yayin wani musayar wuta da 'yan kungiyar asiri su kayi a kwallejin fasaha da ke Auchi a jihar Edo.

Junior Duru kani ne ga mai tsaron baya na kungiyar Lobi Stars, Ebube Duru.

An ruwaito cewa matashin mai shekaru 17 ya gamu da ajalinsa ne yayin da ya ziyarci wani abokinsa a makarantar.

A cewar rahoton, matashin yana daya daga cikin 'yan wasan da aka gayyata domin buga wa Golden Eaglets wasa amma bai yi nasarar samun shiga cikin tawagar da suke buga wasan cin kofin Afirka ta UEFA/CAF na 'yan kasa da shekaru 17 da ake bugawa a kasar Turkiyya ba.

A halin yanzu, yayansa kuma dan wasan Lobi Starsa Ebube Duru ya yi tsokaci kan rasuwar kanin sa inda ya ce ya yi bakin cikin samun labarin rasuwar dan uwansa.

Ya kara da cewa marigayin yana da niyyar zama dan kwallo a rayuwarsa amma yanzu mutuwa ta katse masa hanzari tun yana kuruciyya.

DUBA WANNAN: Wani dan kasuwa ya sheka barzahu bayan kammala 'sukuwa' da budurwarsa a otel

"Abin bakin ciki ne sosai amma dole hakuri zanyi, ina ganin hakan zai sanya in sake dagewa a rayuwata," Ebube ya fadawa footballlive.ng

Ya kara da cewa,"Kafin inyi tafiya ya fada min cewa yana son ya zama kwararren dan kwalo a rayuwarsa, amma yanzu ba zai iya yin hakan ba kuma ina ganin nauyi ya rataya a kai na ganin na zama babban dan wasa da zai yi alfahari da ni."

A halin yanzu, Ebube yana tare da Super Eagles a kasar Senegal inda suke kokarin cin kofin WAFU.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel