Boko Haram: Rundunar soji tayi gum yayinda yan ta’adda suka kashe sojoji da dama a Borno

Boko Haram: Rundunar soji tayi gum yayinda yan ta’adda suka kashe sojoji da dama a Borno

- Har yanzu rundunar sojin Najeriya bata yi magana ba kan rahoton kwanan nan dake zargin cewa yan Boko Haram sun kashe akalla sojoji 14

- An rahoto cewa an kashe sojojin ne a babban hanyar dake tsakanin Gubio da Magumeri a Borno

- Gwamnatin Najeriya ta dage cewa an rage karfin yan Ta’addan Boko Haram

Babu wani jawabi na musamman da kuma tabbaci daga rundunar sojin Najeriya kwana biyu bayan bayyanar wani rahoto dake cewa yan ta’addan Boko Haram a jihar Borno sun kashe wssu sojoji.

Wani rahoto daga Reuters ya bayyana cewa kungiyar Islamic State (IS) ta hannun Kamfanin Dillancin Labaran Amaq tayi ikirarin cewa ta kashe sojojin Najeriya 14 a Borno, yankin Arewa maso Gabashin Najeriya a ranar Laraba, 25 ga watan Satumba.

Majiyar rundunan sojin ta tabbatar da rahoton amman kakakin rundunar sojin bai yi magana ba a lokacin da aka tuntube shi don samun jawabai.

Legit.ng a baya ta rahoto cewa an kashe sojoji da dama yayin da wasu suka bata bayan yan ta’addan sun kai hari kan tawagar rundunar a jihar Borno.

Rahoton ya bayyana cewa majiyar yan banga sun bayyana cewa harin ya faru ne a Karamar Hukumar Gubio dake jihar Borno, musamman akan babbar hanyar dake tsakanin Gubio da Magumeri da misalin karfe 4:15 na yamma.

Har ila yau an rahoto cewa rundunan soji a ranar Laraba, 25 ga watan Satumba tace ta kaddamar da ayyukan Ayem Akpatuma II, Egwu Eke IV da Crocodile Smile IV.

KU KARANTA KUMA: Zargin zamba: A shirye nake na fuskanci Osinbajo a kotu – Timi Frank

Kakakin rundunar sojin Najeriya, Kanal Musa Sagir yace rundunar sojin ta shirya tsaf don gudanar da ayyukan horaswa a yankuna daban daban dake Najeriya.

Musa yace za a kaddamar da operation Ayem Akpatuma II ne a yankin Arewa ta tsakiya da kuma wassu jihohi a yankin Arewa maso yamma - jihohin Benue, Nasarawa, Kogi da Taraba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel