Daga karshe: Hameed Ali ya sanar da sharrudan bude iyakokin Najeriya

Daga karshe: Hameed Ali ya sanar da sharrudan bude iyakokin Najeriya

Shugban hukumar Kwastam na Najeriya, Kwanel Hameed Ali (ritaya) ya ce Najeriya ba za ta bude iyakokinta ba har sai lokacin da sauran kasashen da ke makwabtaka da ita sun kaddamar da dokokin da ke dauke cikin yarjejeniyar shiga da fice na al'umma da kayayyaki na ECOWAS kamar yadda Daily Trust ta ruwaito

A yayin da ya ke magana da manema labarai a ranar Laraba da ya ziyarci iyakar Idiroko na jihar Ogun, Ali ya ce ba za a bude iyakokin Najeriya ba har sai lokacin da sauran kasashen suka cika sharrudan.

Shugaban kwastam din da ya ziyarci wurin tare da Shugaban hukumar shige da fice wato Immigration, Muhammad Babandede ya ce kaddamar da sharrudan shige da ficen kayyayakin zai tabbatar da samun riba da amfani ga dukkan kasashen da ke kasuwanci da juna.

Bayan yabawa jami'an hadin gwiwa da ke aikin tabbatar da dokar na rufe iyakokin, Ali ya ce Shugaba Muhammadu Buhari da kansa ya gamsu da yadda ake gudanar da aikin.

DUBA WANNAN: Wani dan kasuwa ya sheka barzahu bayan kammala 'sukuwa' da budurwarsa a otel

Ya ce, "Muna kai ziyara ga dukkan iyakokin kasar. Kamar yadda ku ka sani muna wani atisaye mai suna 'border drill' hakan yasa muka tura jami'an mu da dama zuwa iyakokin kasar.

"Akwai dalilai uku da suka sa muke kai ziyarar. Na farko shine mu isar da sakon shugaban kasa na yabawa jami'an mu da ke yin wannan aikin.

"Na biyu shine mu sake yin bayyanin dalilan da yasa muke yin wannan atisayen sannan na uku shine sannin kallubale da nasarorin da ake samu yayin gudanar da aikin."

Shugaban na kwastam ya ce shirin daki-daki ake binsa kuma dalilan hakan shine domin tabbatar da yarjejeniya mai kyau da kasashen da ke makwabtaka da Najeriya.

Ya ce za a cigaba da rufe iyakokin har zuwa lokacin da sauran kasashen waje suka amince da zama domin tattaunawa da aiwatar da dokokin da ke cikin yarjejeniyar ECOWAS.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel