Buhari yayi babban rashi na wani abokin karatunsa

Buhari yayi babban rashi na wani abokin karatunsa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna alhini akan rashin wani abokin karatunsa, Dr Tukur Abdullahi, wanda ya kasance likita mazaunin Kaduna, wanda ya rasu a babban asitin kasa wato National Hospital da ke Abuja.

Shugaban kasar yace Dr. Tukur, wanda ya kafa tare da jagorantar asiitin kwararru na Jinya ya kasance mutum mai hallaci, kirki da kuma kula.

“A matsayina na daya daga cikin wadanda suka yi karatu tare da marigayin, a koda yaushe na kan so tarayya da bawan Allan, wanda ya kasance mutumin kirki,” inji Shugaban kasar.

“Marigayi Dr Tukur ya kasance mutum mai tausayi da kuma jajircewa wanda hakan yasa ya zabi fannin likitanci domin yiwa al’umma hidima.

“Mutuwarsa ya taba ni matuka, Allah ya ji kansa ya kuma saka masa da aljanna.

“Allah ya ba iyalansa juriyar wannan babban rashi da suka yi.”

KU KARANTA KUMA: Zargin zamba: A shirye nake na fuskanci Osinbajo a kotu – Timi Frank

Shugaba Buhari ya aika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan Dr Tukur, masarautar Katsina, gwamnati da kuma mutanen jihar kan wannan babban rashi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel