Zargin zamba: A shirye nake na fuskanci Osinbajo a kotu – Timi Frank

Zargin zamba: A shirye nake na fuskanci Osinbajo a kotu – Timi Frank

Wani mai rajjin kare hakkin bil adam, Kwamrad Timi Frank ya bayyana cewa a shirye yake don ganin ya fuskanci mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo a kotu akan zarge-zargen cewa mataimakin shugaban kasar na da hannu cikin badakalar kudi kimanin naira biliyan 90.

Mista Frank wanda ya kasance bako a shirin Channels Television na Sunrise Daily, yace ba zai sauka daga bakansa na danganta Farfesa Osinbajo da hannu a badakalar ba.

Tsohon mataimakin babban sakataren na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a baya yayi kira ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Darektan hukumar tsaro na sirri (DSS), hukumar ICPC, da su yi bincike kan ikirarin da yayi na cewa mataimakin shugaban kasar ya karbi kudaden da ake magana a kai daga hannun hukumar dake tattara kudaden shiga (FIRS) don daukar nauyin zaben shugaban kasa da ya gabata.

Frank ya kalubalanci Farfesa Osinbajo da ya kai karar shi kotu akan zargin, kalubalen da mataimakin shugaban kasar ya dauka ba da wasa ba.

Yayin da yake mayar da martani kan zargin, mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa a shirye yake ya ajiye kariyar da kundin tsarin mulki ta bashi don wanke kansa daga zargin.

Osinbajo ya bada umurnin fara shirin daukar mataki akan Timi Frank, da kuma wani mai suna Katch Ononuju wadanda suka sanya sunayensu a zargin.

Yayin da yake magana akan matakin da mataimakin shugaban kasar ya dauka, Mista Frank yace jawabin da ya gabatar a ranar 23 ga watan Satumba ya tsaya a matsayin gaskiyar sa.

KU KARANTA KUMA: Babu wani shiri da ake na tsige Sarki Sanusi – Gwamnatin Kano

Yace zamanin zalunci da tsoratarwar jami’an gwamnati ya kare kuma saboda haka, a shirye yake ya fuskanci mataimakin shugaban kasar a kotu.

Tsohon kakakin na APC yace ba zai bayyana shaidunsa ba yanzu amman zai jira har sai idan lokaci yayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel