Bakin talauci ya sanya Ikechukwu azumin kwanaki 41, in ji mahaifiyarsa

Bakin talauci ya sanya Ikechukwu azumin kwanaki 41, in ji mahaifiyarsa

- Yaro mai shekaru 19 ya haye wani tsauni a garin Abakaliki inda ya yi kwanaki 40 yana azumi da addu'a

- Mahaifiyar Okechukwu ta bayyana ccewa tsananin talauci ne da rashin da suke ciki ya sa yaron aikata hakan

- Yana da burin zama lauya nan gaba amma ya hango kalubalen da ke tunkarosa sanadin rashin kudin danginsa

Mahaifiyar yaro mai shakaru 19, Ikechukwu Oke, wanda ya yi azumin kwanaki 41 ta bayyana dalilan da suka sa yaron nata ya haramtawa kansa ruwa da abinci na tsawon lokacin nan a hira da tayi da wakiliyar jaridar Punch.

Ikechukwu mai shekaru 19 a duniya ya yi azumin kwanaki 41 sakamakon mugun talaucin da ya addabi danginsa.

Yaron mai shekaru 19 a duniya yana aji 4 ne na makarantar sakandire a Ishieke, Abakaliki.

Yana da burin zama lauya a rayuwarsa amma sai yake hangen kalubale wajen yuwuwar cikar burinsa.

KU KARANTA: An-kama-wani-mutum-mai-damfara-da-sunan-manajan-sashin-kudi-na-nnpc

Ya bar gida da niyyar komawa wajen mahaifiyarsa daga ziyarar da ya kaiwa babban yayansa. Mahaifiyarsa ta tambayi yayan nasa bayan da aka shafe kwanaki Ikechukwu bai isa gida ba.

Tuni hankula suka tashi aka bazama neman Ikechukwu. Sai bayan kwanaki 41 aka samesa a wani tsauni inda ya zauna a nan yana azumi.

Da manema labarai suka tambayi mahaifiyarsa akan ko ta san dalilinsa na yin hakan? Sai ta ce, "Ikechukwu ya yi azumin nan ne don tsabar bakin talaucin da ya addabemu. Yana da burin zama lauya nan gaba amma yana hango rashin yuwuwar cikar burinsa sakamakon talaucinmu,"

"Tunda mahaifinsa ya rasu a 1996, muka samu kanmu cikin wannan halin. Yayansa ne ya sanyasa makaranta don ganin cikar burinsa," in ji ta.

Ta kara da cewa, "Nakan yi kananan aiyuka har da leburanci inda nakan samu N1,400 a rana. Da shi muke ci da sha tare da sauran bukatunmu ni da yarana. A wajen aiyukan ne na kusan rasa hannuna daya watarana."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.

Asali: Legit.ng

Online view pixel