Wani dan kasuwa ya sheka barzahu bayan kammala 'sukuwa' da budurwarsa a otel

Wani dan kasuwa ya sheka barzahu bayan kammala 'sukuwa' da budurwarsa a otel

Wani dan kasuwa mai suna Onyekachi Nwosu ya mutu yayin da ya ke saduwa da masoyiyarsa mai suna Chima a unguwar Aguda da ke Surulere a jihar Legas.

Punch Metro ta ruwaito cewa Nwosu da Chima sun ziyarci wani otel mai suna Alfredo Suites misalin karfe 10 na dare domin su dan shakata amma bayan wani dan lokaci sai mutumin mai shekaru 36 ya fara numfashi 'sama-sama'.

Hakan yasa masoyiyarsa Chima ta ruga waje da sanar da ma'aikatan otel din abinda ke faruwa da niyyar a kai masa dauki.

An gano cewa manajan otel din, Uche Ejionye tare da wasu ma'aikatansa sun garzaya dakin amma sai suka tarar cewa Nwosu ya ce ga garin ku.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa daga bisani 'yan sanda sun kama ma'aikaciyar otel din mai suna Mary da masoyiyar marigayin wato Chima domin zurafafa bincike kan dalilin rasuwar mamacin.

Ejionye ya ce wani ma'aikacinsa Isaac ne ya sanar da cewa halin da Chima ke ciki kuma suka garzaya dakin otel din suka tarar da gawar Nwosu.

DUBA WANNAN: Miji na yana neman yin asiri da ni: Matar aure da fadawa kotu

Manajan otel din ya ce, "Ina tare da wasu baki ne sai Isaac ya shigo ya fada min cewa Chima tana neman taimako. Da na tambaye ta sai tace babu lafiya kuma ni da mai gadi muka tafi dakin muka tarar da gawar Nwosu zindir a kwance.

"Da na tambaya mene ya faru sai Chima ta ce sun gama saduwa da Nwosu amma daga baya sai ya fara makwarkyata hakan ya sa ta rugo waje domin neman taimako. Na fada mata ya mutu kuma na kira DPO din 'yan sanda na Aguda shi kuma ya ce kar mu bari ta tafi.

"Da yan sandan suka iso, sun kama ma'aikatan otel din biyu da suka bawa Chima da Nwosu daki amma na raka su zuwa ofishin 'yan sandan inda muka bayar da shaidan abinda ya faru sannan daga bisani ni da mai gadin otel din muka koma muka kai gawar mamacin zuwa asibiti misalin karfe 2 na dare."

Wata majiya da tayi magana da Punch Metro ta ce iyalan mamacin ba za su shigar da kara a kotu ba domin likitansu ya gudanar da bincike kan gawar mamacin inda ya ce bugun zuciya ne sanadin rasuwar Nwosu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel