Kotu ta tsare mutumin da ya kashe mahaifiyarsa da hannunsa ta hanyar fille mata kai

Kotu ta tsare mutumin da ya kashe mahaifiyarsa da hannunsa ta hanyar fille mata kai

Wata kotun Majistare ta jihar Ebonyi da ke zama a Abakaliki ta tsare wani mutumi dan shekara 27, Monday Otubo, a gidan yari kan zargin kashe mahaifiyarsa, Comfort Otubo.

An tattaro cewa mai laifin ya aikata ta’asar ne a ranar 22 ga watan Satumba, 2019, a kauye Ndufu Amaezekwe da ke karamar hukumar Ezza ta kudu na jihar.

Anyi zargin cewa mai laifin ya fille kan mahaifiyar tasa.

An gurfanar da wanda ake zargin a ranar Litinin, 23 ga watan Satuumba, kan tuhuma guda na kisan kai.

Dan sanda mai kara, Inspekta Mbam Chinedu, ya fada ma kotun cewa hukuncin laifin na kunshe a sashi 319 (1) na dokar laifi, Cap 33, Vol. 1, dokokin jihar Ebonyi, 2019.

Tuhumar ya zo kamar haka: “Cewa kai, Monday Otubo, a ranar 22 ga watan Satumba, 2019, a Ndufu Amaezekwe da ke karamar hukumar Ezza ta kudu, karkashin wannan kotu, ka aikata ta’asa ta hanyar fille kan wata Comfort Otubo da adda.”

KU KARANTA KUMA: Babu wani shiri da ake na tsige Sarki Sanusi – Gwamnatin Kano

A wani lamari na daban, mun ji cewa wata mata mai suna Nkeiruka Cynthia Kamalu, ta bayyana yadda dan majalisa, Uju Kingsley Chima ya kwanta da ita a shekarar 2015.

Chima dai dan majalisa ne na tarayya mai wakiltar Ohaji/Egbema, Oguta da Oru ta yamma dake cikin jihar Imo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel